Akan Springster

Maraba da zuwa Springster! Wajan da ‘yan mata zasu hade, suyi koyo kuma su walwala kan su! Kiyi Imani da kanki domin mun riga munyi…..

Kuma muna da kundin sakonnin springster, da kuma ganarwa na tsira da zai taimake mu zama abu mai inganci.

Kundin sakonnin springster

  1. Kowane mutum springster ne: Babu doka akan wanda zai iya, ko ba zai iya zama springster ba. Kowane mutum zai iya hade
  2. Koda yaushe a tare, baza ki kasance ke kadai ba: Zamu iya amince da juna saboda abun da yan springster suke yi kenan.
  3. Ku rarraba kauna:Kada kuji kunya! Gaya mana labarin ku! Muna nan saboda mu goya muku baya kuma muyi shagali da juna.
  4. Ki cigaba da imani: Idan lokaci ya kara tauri muna samun goyon bayan abokai, da iyalai da kuma al’umma- Bamu fidda rai
  5. Ki sa kai kiyi aiki: Babu wani tsafi ta hanyar samun nasara, yana daukan himma da tsaari
  6. karya katangan wariyar nan: Kada ki yarda wani ya sa miki makura akan abun da kike son ki samu nasara a kai a rayuwa
  7. Cigaba nishadi: Himma nada muhimmanci. Amma kada ki manta kiyi nishadi kuma.
  8. Da zaran kika zama springster, zaki ci gaba da zama springster: Ke springster ce har a bada. Duk inda kika je, za’a miki maraba.

Ki rarraba kundin sakonnin springster