Na kankanta na fara samun kudi?

Ku koya yadda Amara ta fara samun kudi da wuri

Shekarun Amara goma sha shida a lokacin da ta fara samun kudi.

Bata tsammanin zai iya faruwa ba har sai data karanta wani labari a wani mujalla.

Akan wata mace ce da aka bawa lambar girmamawa na karamar miliyoniya a Afirka. Shekarun ta ishirin da takwas.

Wannna labarin ya saka Amara tunani akan hanyoyin da zata iya fara wani kasuwanci ko samun kudi.

Duk da haka, bata tabbata yadda zata fara ba. Sai tayi wa makwaficiyar ta dake sana’ar dinki magana.

Amara na sonta ta koya mata akan yin kasuwanci. Abun ya bawa matan mamaki. Duk da haka, ya burge ta da Amara ke son ta fara da sauri. Ta tambaye Amara dalilin daya sa take son tayi.

Amara ta gaya mata cewa tana son ta gyara rayuwar ta.

Matan ta bawa Amara shawara. Tace “ Ki nemo wani abu da kike so sai kiyi shi.

Idan kika fara samun kudi, ki tabbata cewa kin yi ajiya.

Kiyi setin wani muradi akan nawa kike son kiyi ajiya a kowane mako ko kuwa wata daga abun da kike samuwa.

Zaki iya amfani da wannan ajiyar ki siyo wani abu da kike butaka ko kuwa ki kara fadada kasuwancin ki.

Ki tuna ki tsirata kana idan kika hadu da abokan kasuwancin ki.”


Amara tayi tunani akan abubuwan da take kaunar yi sai ta yanke shawarar fara yin dutsen ado. Wannan abu ne data koyar wa kanta.

Ta fara da yin wa abokan ta dutsen ado a kyauta.

Wata rana yar uwar mahaifiyarta ta siya na duba daya da dari biyar (N1500). Abun ya bawa Amara mamaki.

Abokiyar yar uwar mahaifiyarta taga sarkar wuyar. Tace mata tana son biyu. Abun ya saka Amara jin dadi yadda sana’ar ta ya kasance. Har abokan ta ma sun fara siya.

Shekara daya ya wuce tun da Amara ta fara kasuwancin ta. Yau tana da abokan kasuwanci da yawa. Kuma ta yanke shawarar koyar da sauran yan mata a al’ummar su yadda zasu yi dutsen ado.

Amara ta tsara bude shago a nan gaba. Kuma tana son ta bude cibiyar horaswa domin ta kara koyar da yan mata.

Baku kankanta ku fara samun kudi ba. Ku zabi wani abun da kuke son yi sai ku fara aiki akan sa. Koda abun da kuke so ba abun da kowane mace zata yi bane kamar gini, ko yin aski. Kuyi imani da kanku da abun da kuke so.

Kuma ku tuna ku tambaye wani amintaccen mutum ya baku shawara akan abun yi.

Kun riga kun fara samun kudi? Gaya mana yadda kuka yi a wajan sharhi. Sauran Yan Springster zasu so su koya daga wajan ku;x;x

Share your feedback