Jerin abubuwa da zaku iya yi: Akwatin kayan ado (sarka, dan kunne, warwaro)

Wani wuri na musamman da zaku ajiye abubuwan ku masu daraja

Dukkan mu mun san akan akwatin kayan ado na katako ko kuwa gilashi. Wadannan abubuwan nada kyau amma suna da wuyan yi.

Me zaku ce idan muka gaya muku cewa zamu iya hada muku wani akwatin kayan ado mai kyau a sa’a daya. Kuma zaku yi sa da fallen takarda da kuma kyallen atamfa.

Kun kosa ku san yadda ake yin sa? Kuna shirin yadda zaku hada ku siyar wa abokan ku? Toh ku duba dabarun a nan kasa.

Ga abubuwan da kuke bukata:

  • Kyallen atamfa (zai iya zama wani tsohon zani)
  • Gam
  • Wani tsohon kwalin falen takarda
  • Almakashi
diy1.jpg

Mataki na daya
Ku yanke saman kwalin falen takardar domin yayi kama dana hoton nan a kasa.

diy2.jpg

Mataki na biyu
Ku baza atamfan a kasa sai ku saka kwalin falen takardar a samar sa. Ku kula ku saka kwalin falen takardar a cikin gefen kyallen. Ku tuna ku yanke bakin kyallen. Ku tabbata cewa kun samu murabba’i babba da zai rufe dukka kwalin bayan kun yanke bakin kyallen.

diy_3.jpg

Mataki na uku
Yin amfani da kwalin a matsayin ganarwa, ku yanke bakin kyallen a kowane gefe. Wannan zai saka shi sauki a ninka kyallen cikin kwalin.

diy4.jpg diy_5.jpg diy6.jpg diy_7.jpg

Mataki na hudu
Ku saka gam din a gefen ciki da waje kwalin. Ku ninka kyallen saboda kowane gefen kwallin ya rufu. Ku danna kyallen a kwalin da hankali saboda ya mannu. Zaku iya barin kyallen a cikin kwalin, amma ku tabbata kunyi sa da tsafta.

diy8.jpg diy9.jpg diy10.jpg diy11.jpg

Mataki na biyar
Ku maimaita wannan matakin har sai kyallen ya rufe dukka sassan.

diy12.jpg diy13.jpg

Da zaran kun gama, ku tabbata kun bari ya bushe da kyau.

diy14.jpg

Shikenan! Akwatin kayan adon ku ya shirya domin amfani.

diy15.jpg diy16.jpg

Kun san abu mafi kyau? Zaku iya samun kudi daga wannan.

Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya samun kudi da wannan kwarewar!

Na farko, zaku iya sa abokan ku su biya ku naira dari domin ku koya musu yadda zasu yi.

Ko kuwa zaku iya saida wa abokan ku, ko kuwa sauran mutane a al’ummar ku. Idan kuna son ku san nawa zaku saida, ku lissafa nawa kuka kashe domin ku hada daya, sai ku kara dari biyu a sama, shikenan kun samu farashin.

Ga misali, idan abubuwan da kuke bukatan hada akwatin dari uku ne, ku kara dari biyu a sama, sai ku saida a dari biyar.

Kun taba hada wasu abubuwa da kuma kuka saida? Ku gaya mana akan sa a wajan sharhi a nan kasa. Wanne abubuwa ne kuma zaku so ku koya?

Share your feedback