Domin samun wannan walkiyar
Idan zaku je makaranta, ko gidan yan uwan ku, ko kuwa wani taro, me kuke yawan dubuwa?
Tsaftar gashi da kuma tsarin gashi?
Tsaftar kaya?
Tsaftar yatsu?
Takalman ku fa, kuna tabbata cewa suna da tsafta da kuma walkiya?
Idan kuka ce eh, toh wannan aikin naku ne.
Zaku so wannan abun goge takalmin. Yana da saukin yi kuma kuna bukatan abubuwa guda uku ne kawai domin kuyi sa.
Idan abokan ku suka ga yadda takalman ku ke walkiya, mai yiwuwa zaku iya siyar musu ko kuwa ku fara wani ajin koyarwa a kyauta.
Abun da kuke bikata
Yadda zaku yi sa
Mataki daya
Ku matse dukkan ruwa daga lemun.
Mataki na biyu
Ku cire dukkan irin shuka da kuma sauran datti daga ruwan lemun.
Mataki na uku
Kuyi amfani da murfin kwalban man zaitun ku ku auna ruwan lemun so biyu. Ko kuwa zaku iya auna cokali biyu na ruwan lemun. Ku saka shi a karamin kwanan ku mai tsafta.
Mataki na hudu
Kuyi amfani da murfin man zaitun ku ku auna man zaitun so biyu. Ko kuwa zaku iya amfani da cokali ku auna so hudu. Ku hada shi da ruwan lemun dake cikin kwanan.
Mataki na biyar
Ku hada ruwan lemun da man zaitun sai ku juya shi sosai.
Shikenan!!!
Yadda zaku yi amfani
Mataki na daya
Ku tsoma wani kyale mai tsafta a cikin abun goge takalmin. Sai ku bar takalmin na minti kadan.
Mataki na biyu
Kuyi amfani da tsummar ku goge takalmin (wannan yana nufin cewa goge shi da takalmin da karfi saboda yayi kyalli da kyau)
Ga takalmin kafan a goge….
Sai kuma gashi nan bayan da aka goge…
Abubuwa da yakamata ku tuna
Zaku gwada wannan abun goge takalmin? Ku rarraba damu a sashin sharhi.
Share your feedback