Yadda zaku ji dadin shekarun ku na matashi

Kananan abubuwa ne suka fi muhimmanci

Wasu lokuta kuna kosa kuyi girma da wuri. Kun kosa kuyi abun da kuke so, a lokacin da kuke so.

Amma ga gaskiyar: baza ku kara zama matasa ba kuma.

Wannan ne daya daga cikin lokuta a rayuwa mafi inganci. Kada ku dame kanku sosai akan yin girma da har zaku rasa dadin dage cikin zama matasa.

Wannan ne lokacin da zaku gane kanku da kuma abun da kuke so.

Domin fara fadin abun dake ran ku da kuma tsayawa da kanku. Kun shirya yin nishadi? Toh muje zuwa:

Ku runguma sabon jikin ku
Ku kali madubi ku so sabon jikin ku. Kuyi murna da nonuwar ku, da cinyoyin ku, kuma eh ku so al’adar ku, na halitta ne kuma na musamman. Halittar ku nada kyau. Bani biyar, yarinya!

Zuba jari a abokan kwarai
Kuce a’a wa jabun abokai ko kuwa mutane dake saka ku jin bakin ciki game da kanku. Wannan ne lokacin da zaku nemo mutane dake kaunar ku kuma ku gina abokantaka da zai dade har abada. Ku nemo mutane dake son ku a yadda kuke kuma dake girmama ra’ayin ku. Zasu goya muku baya sai kuma ku goya musu baya.

Ku tuna, kauna zai iya zama abun nishadi
Yin soyayya daya ne daga cikin abubuwa dake tare da yin girma. Ba komai bane idan kuna nan da wani dake kaunar ku da gaske kuma dake bi daku a yadda ya dace. A gaskiya, zai iya zama abu mai burgewa. Mu walwala muyi nishadi.

Kada kuji tsoron samun babban buri
Burin ku nada inganci. Kada ku yarda wani ya gaya muke daban. Kuna son ku samu naku sana’a? Ko ku samu maganin cutar ciwon daji? Ko ku tashar da jirgin sama wata rana? Kuyi sa! Tare da aiki sosai da kuma kwazo, zaku iya yin komai.

Kuyi dariya sosai, kuma ku wautawa
Kada ku dauka komai da zafi. Idan kuka fada a kasa, ku tashi kuyi dariya. Kun tuna wani abu mai ban dariya? Ku sake kuyi dariya. Lokuta kamar haka ne ke saka rayuwa daraja.

Menene sauran hanyoyi da zaku ji dadin kasancewa matasa? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback