Ku tsaya da karfin ku idan ana matsa muku lamba
Shekarun matashin ku babu matsala ko? Zaku samu sabobin abokai kuma ku koya sabobin abubuwa. Bayan duke, kun gano cewa maza basu bace ba!!!
Amma abun shine, duk da kuke sha’awar samari, ba lallai sai kunyi soyayya ba idan baku shirya ba. Ba dole bane. Saboda haka, idan wani yaro yace yana son ku kuma baku son sa, ku ce a’a. Kuyi masa magana da hankali amma kuyi tauri. Kuna da daman samun naku ra’ayi.
Babu komai a cikin zaman kadaici. Kuna da isashshen lokaci da zaku yi soyayya. Saboda haka, ku dauke lokacin ku yan mata. Baku bukatan cewa eh saboda kowa na yi. Idan baku bi jama’a ba, zai sa ku zama masu na musamman kuma babu kamarku.
Cewa a’a zai iya yin wuya. Mai yiwuwa baku son ku bata musu rai. Ko kuwa baku son abokan ku suce kuna da tauri ko kun cika zabi. Amma mai yasa baza ku gamsar da kanku ba domin kuna son ku gamsar da sauran mutane? Farin cikin ku yazo farko. Koda yaushe ku amince da ilhamar ku kuma ku yarda da kanku.
Wasu lokuta idan kuka ki fita da wani yaro, bazai bari ya wuce haka kawai ba. Zai fara aikata wasu irin halayye domin ya canza muku ra’ayi. Mai yiwuwa ma ya fara matsa muku lamba kowane rana! Amma wannan baya nufin cewa yana kaunar ku. Mai yiwuwa kawai yana son ya bunkasa girmar kan sa ne. Kuma kuna da kaifi sosai ace ku yarda da wannan.
Wani abu kuma: Idan baku son wani yaro, kada ku fita dashi don kuna tausayin sa. Bai dace ba. Kada kuji kunyar cewa a’a. Ku tsaya da gaske ku fadi ran ku. Ku tuna, idan yaron ya fara yin muku barazana ko takura muku, ku kai rahoton sa a wajan wata ko wani amintaccen babban mutum nan take. * Kun taba kin wani saurayi? Me kuka gaya masa? Ya ya kasance? Gaya mana a nan kasa.
Share your feedback