Koya sanin lokacin da zaku kashe kudi da kuma lokacin da zaku yi ajiya
Wasu lokuta yana mun wuya nace wa abokiyata Ada a’a idan tana son mu siya kayan kwadayi ko kuwa mu siya wani takalmi mai kyau.
Na san mutane na fadin cewa babu komai cikin son lalata kanka a wasu lokuta. Amma yana da muhimmanci a gane cewa lalata kanka yanzu na iya saka mutum asarar wani abu mafi inganci a nan gaba.
Toh ya zan san abun daya kamata na kashe kudi na akai?
Kafan na kashe kudi akan wani abu, dole na tambaye kaina ko ina bukatan wannan abun. Ga misali, akwai wasu lokuta da nake ji kamar dole sai na siya wani takalmi dana gani a wani waje (musamman idan ina da wani biki dake zuwa). Amma dole sai na tambaye kai na ko ina bukatan sa ko kuwa ina son sa ne kawai.
Bukatu abubuwa ne da baza mu iya rabuwa da ba - kamar abinci mai lafiya, takalmar makaranta, magunguna. Abun da ake so kuma, abu ne kawai da ake so amma ba’a bukata! Abubuwa ne da zamu so mu samu amma kuma zamu iya rayuwa ba tare dashi ba.
Abokiyata Ada na kirar kayan da take siya kamar yan kunne, jari. Amma, haka ne? Yan kunnen Ada sunyi kyau yau amma mai yiwuwa zata iya amfani dasu na watani kadan ne kawai.
Jari masu kyau sune zasu iya amfana ku na watani da yawa.
Jari mafi kyau sune abubuwan nan da zasu iya canza rayuwar ku. Abubuwa kamar horar kwamfuta ko kuwa kudin makaranta. Wadannan ne abubuwan da mai yiwuwa muke bukatan yin ajiya wa.
Saboda haka a maimakon siyan wani abun yayi da ba zai dade muku ba, kuyi ajiya ku siya wani abu da kuke bukata.
Wannan yana nufin cewa a’a wa wannan takalmin, ko riga, ko kuwa wanann akwatin kayan ado.
Zaku yi nasara a karshe. Zaku yi alfahari da kanku idan kuka fara samun kudi kuma kuka cimma burin ku.
Kuna son ku fara yin ajiya? Ku karanta wannan makalar
Meyasa kuke ganin kuna bukatan yin ajiya? Ku rarraba dalilan ku damu a wajan sharhi.
Share your feedback