Sabo Da Ilimi Zai Iya Haskaka Rayuwaeki a Gaba!
Wasu lokuta makaranta na iya zama ƙalubale, kuma zai iya zama da wahala ɗaukar darussa daban daban Amma ki sani tushen ilimi mai zurfi zai taimaka miki shiga duniya domin cimma burin ki. Idan ba kya zuwa makaranta, nemo wani shiri ko wajan horarwa ko wani wanda zai iya taimaka miki koyon ki kware a kan wani abu domin cimma burinki. Nemo wani abin alfahari wanda zai zama abin koyi a gareki, malami ko iyaye. Nemi taimako da shawarwari yayin wannan tafiya.
Buri wani abu ne wanda ke da kanki ki ke so ki cimma a rayuwa. Yana da matuƙar mahimmanci ki nemi burinki a rayuwa. Wannan hanya, za ki iya ƙirƙirar hanyoyi wanda za ki yi aiki da su zuwa ga cimma wanan burin. Riki littafin rubutu tare da ke domin rubuta burikanki a waje guda. Ki bin cika ki gani ko yaya.
Shimfiɗa bururruka da za su ƙarfafa miki gwiwa kuma su karfafa wajen aikin makaranta da koyo. Ki na son sami nasara? Ki dinga zama na daya a aji? Ko ki inganta sakamakonki? Ki dinga rubutu kuma kina karanta shi a koda yaushe.
Share your feedback
Tunanin ku
Inaso nazama likita
March 20, 2022, 8:04 p.m.