Farin ciki a cikin dakikoki guda sitin
Kamar yanayin gari, shaukin mu na canzawa. Minti daya muna farin ciki akan rayuwa sai kuma minti na gaba muna bakin ciki.
Kuma wasu lokuta, zai iya dan wuya mu juya daga bakin ciki zuwa farin ciki. Amma zaku iya.
Kuna al’ajabin yadda zaku juya fushi zuwa murmushi?
Toh ga hanyoyi masu nishadi guda uku…..
Dabara na daya- Sidabbarun jirgin sama
Idan kuka kara fushi akan wani abu. Ku tashi sama, ku kirga daga biyar zuwa daya sai ku wayence kamar ku jirgin sama ne da zai tashi.
Kamar haka: Biyar…..Hudu….Uku...Biyu...Daya… sai kuce TASHI!
Idan kuka ce “Tashi”, kuyi tsalle. Ku motsa jiki ku girgiza dukka abubuwan nan mara kyau. Jin wakoki da kuma yin rawa hanyoyi ne masu kyau da zaku iya farawa. Wannan dabarar zai taimake ku idan kuna bukatan karfafa gwiwar yin wani abu mai muhimmanci.
Dabara na biyu- Ku rubuta shi sai ku yaga
Ku samu fallen takarda ku rubuta duka abubuwan nan mara kyau da kuke ji. Mai yiwuwa wani ya bata muku rai kuma kuna bakin ciki. Bai kamata ku rike wadannan abubuwan a zuciya ba. Ku rubuta su a fallen takardar sai ku yaga takarda.
Hankalin ku zai kwanta saboda kamar wadannan abubuwan mara kyau da kuke ji basu da iko a kan ku kuma ne.
Dabara na uku- Madubi a kan bango
Kalmomin ku nada iko. Kun san cewa tunanin ku na sanadiyar shaukin ku kuma shaukin ku na sandiyar halayar ku? Shiyasa yake da muhimmanci kuyi tunani masu kyau kuma ku fada abun dake zuciyar ku.
Saboda haka, kowane safe idan kuka tashi, ku kalli kanku a madubi sai ku maimaita wadannan kalmomin:
Ina kaunar kaina
Ina da karfi
Ni isa
Ana kauna na
Ina da daraja
Ina da kyau
Ina da kaifi
Rayuwa na nada manufa
Zan iya cimma burina
Ku tuna, ba wanda ke farin ciki kowane lokaci. Idan kuna bakin ciki, yana da kyau ku amince da yadda kuke ji kuma kuyi kokari ku gwada daya daga cikin dabarun nan domin ku wuce nan. Ko kuwa zaku iya yin magana da wata abokiyar ku ko wata amintaccen babba. Mai yiwuwa su taimake ku.
Me kuke yi idan baku jin dadi? Ku rarraba dabarun ku damu a sashin sharhi.
Share your feedback
Tunanin ku
Sanya nishadi abu ne mai kyau ga al-ummah, yadace iyaye,masoya mudinga sanya yan uwan mu parinciki
March 20, 2022, 7:54 p.m.