Yadda zaki yi nishadi a ranar ki
kasar Naijeria a rana ishirin da bakwai ga watan Mayu. Wannan yana nufin cewa babu makaranta kuma gaba dayar ranar na yin shagali ne. Na san kuna murna akan wannan ranar.
Kun san akwai abubuwa da yawa masu amfani da zamu iya yi a ranar.
A nan kasa akwai wasu abubuwa na shagali da hanyoyi masu amfani da zamu iya kwashe lokaci muyi a ranar yara;
Ziyarta wani tsohon dangi
ki bawa kakannin ki, ko dan uwa da yar uwar iyayen ki da kika dade baki gani ba mammaki, ki zaiyarta su.
kada ki jira sai kuna da taro na dangin kafan ki gansu.
Kwashen lokaci da wani babban dan dangin ku zai iya zama wani hanyar koyan abubuwa masu muhimmanci. Suna yawan samun sabobin abubuwa da zasu koya wa yan kasa dasu.
Ki kwashe lokaci da abokan ki
Zamu iya yin shagali da abokan mu. Mu san me suke yi tunda mun dade bamu hadu ba. Zamu iya ziyarta gidajen su.
Ki tabbata cewa kin tsira kuma akwai wani babba da kika yarda da daya san inda zaki je.
Ki kwashe lokaci da iyayen ki
Zamu iya jin dadin kwashe lokaci da Iyayen mu. Zaki ga cewa baza su gajiyawa ba kamar yadda kike tunani.
Zamu iya zuwa wajajen da ake yin shagali dasu. Zamu iya kwashe lokaci dasu a gaba dayar ranar muna labari dasu akan abubuwan da suke son yi da safgar su.
Muyi tunanin yadda zasu yi murna idan muka yanke shawara cewa zamu kwashe lokaci dasu kuma muyi shagali dasu.
Ki ziyarta wani sannanen waje a al’ummar ki
ki ziyarta gidan ajiye dabbobi, ko gurin da mutane ke zama suna shan iska, ko wani wajan siyan kaya, da sauran su. Ya dangantaka da irin wajen da kike zama.
Zamu iya ziyarta irin wajajen nan da abokan mu, ko yan uwan mu, ko yan dangin mu.
Ki tabbata akwai wani babba da ya san inda zaki je kuma lokacin da zaki dawo.
Kiyi aikin agazawa mutane
Zamu iya yin wani abu mafi kyau ma wasu a ranar.
Zamu iya ziyarta wani asibiti ko gidan marayu ki bayar da tallafin kayan mu da bama amfani, ko kayan wasan yara harda takardu wa sauran yaran.
Zaki iya sa kai ki taimake tsaftace gidan wasu tsofofi da ke zama a al’ummar ku.
Kin tsarar da wasu abubuwa da kike son kiyi a ranar yara? ki gaya mana a shafin sharhin mu.
Share your feedback