Koda yaushe ki zama abokiya mafifici wa babban abokiyar ki

Ba yanzu kawai ba, amma har abada

Mai yiwuwa kina da wani babban da’irar abokai.

Amma akwai dan kadan da zaki iya amince da sirrin ki masu zurfi. Sune mafificin abokan ki.

Gaskiyar shine, mafificin abokiyar ki yau zata iya daina zama abokiyar ki gobe.

Koda yaushe abokantaka na daukan aiki. Dukka abokantaka na bukatan lura.

Idan baku yi hankali ba zaku rasa abokantakan.

Kin taba asarar mafificin abokiya? wannan babban bala’i ne!

Ga hanyoyi da zai taimake ki cigaba da zama mafificin abokiya.

Kada kiyi takara

Kema dai dai kina da kyau da kuma kwarewa. Baku bukatan jin kishin juna. Mai yiwuwa babban abokiyar tafi ki iya wani abu, amma akwai wani abu da kema kika fi iya wa.

Ku riga fadin gaskiya

Yawancin mutum na tunanin cewa “yi hakuri” ne kalma mafi wuya. Fadin gaskiya kuma daga zuciya yafi wuya. Ki zama mai fadin gaskiya amma banda raunata da kalmomi. Ga misali, idan abokiyar ki ta tambaye ra’ayin ki akan sabon gashin ta, kada ki gaya mata baki so shi. Kawai ki gaya mata abu kamar “ Naga alama kina gwada wani sabon kamani, amma bari na nuna miki wani salo mai kyau da zaki iya gwadawa bayan wannan.” Wannan na nuna cewa kina gaskiyar ra’ayin ki ba tare da raunata ta ba.

Ku yabe juna

Ku yabe juna da gaskiya. Wannan baya nufi cewa dole sai kun yabe komai. Amma kowa nason yaji wani kalma mai dadi koda yaushe. Abokai na maida hankali da juna, koda wani karamin abu ne.

Kuyi shagali tare

Abokiyan kwarai na mura cin nasaran abokan su. Abokiyar ki ce dalibi mafi ilmi a ajin ku? Ku taya su murna kuma ku shagali dasu. Wannan yana nufin cewa komai da abokan ku ke aiki akai. Sunyi aiki sosai domin su samu wannan sakamakon. Kuyi shagali dasu.

Makullin abokantaka mai karfi shine goyon bayan juna da kuma kasancewa muna nan kusa idan suna bukatan mu.

Shine bambanci a cikin babban abokiya da kuma babban abokiya na har abada.

Gaya mana akan abokan ki ko kuwa babban abokan ki a sashin sharhi.

Share your feedback