Kwarewa masu ban mamaki da kuke da

Muryan ku nada muhimmanci

Kuyi tunanin wani yana yanke shawara akan irin wakokin da zaku ji, irin rigar da zaku saka, ko kuwa darasin da zaku dauka a jami’a.

Wannan al’amarin ne yawancin mu ke samun kan mu a ciki.

Muna ji kamar ra’ayin mu bai da muhimmanci.

Muna yawan ji daga iyalai da abokai cewa yakamata yan mata nada hankali, suna magana da natsuwa kuma basu fadin abun dake ran su.

Saboda haka yawancin lokuta muna kasa yin magana.

Amma muna son mu gaya muku cewa mace nada yancin yin magana. Kuma zata iya yin sa da hankali da kuma natsuwa.

Kuna al’ajabin dalilin daya sa da kuma yadda zaku yi magana? Toh muje zuwa:

Yan mata nada ra’ayi suma!!!

Abun mamaki ne wai zamu iya fadin komai idan muna tare da abokan mu, amma muna kasa magana a cikin jama’a. Muna tsoro kada a mana dariya. Amma a gaskiya, ko da yake muna da ra’ayi dabam, ra’ayin ku ma nada muhimmanci. Kuma, mai yiwuwa fadin ra’ayin ku zai canza zuciyar wani. Abun muhimmancin shine ku san abun da kuke son ku fadi, dalilin daya sa kuke son ku fadi, da kuma fadin sa da ladabi.

Ku wayence kamar kuna da tabbaci har sai ya zama da gaske

Yin magana a cikin jama’a na bukatan tabbaci. Eh bai zuwa da sauki koda yaushe. Amma zaku iya kokari koda kuna tsoro. Gaskiyar shine ba wanda zai iya sanin abun dake ran ku. Abun da zasu gani shine wata mai tabbaci sosai da zata iya magana. Kuma idan kuna gwaji sosai zai zo muku da sauki. Bada jimawa ba, zaku ga kun kara samun tabbaci!

Kada ku bari wani abu ya sanyaya gwiwar ku

Idan kuna tsoro ko kuwa kuka manta da abun da kuke son ku fadi, kada ku sanyaya gwiwar ku. Zai iya faruwa da kowa. Amma ku tsaya da karfi, abubuwa zasu yi sauki da lokaci.

Ku tuna, akwai abubuwa da yawa da mu yan mata ke yi kowane rana da zai nuna karfin mu. Saboda haka, a yayin da yin magana a cikin jama’a zai kasance da wuya, kuna da zuciyar yin sa.

Kun taba samun kanku a wani al’amarin daya saka ku ji kamar ra’ayin ku bai da muhimmanci? Ya kuka ji? Me kuka yi? Ku rarraba da mu a sashin sharhi.

Share your feedback