Bayanin kungiyar abokantaka

Koda yake mun banbanta da juna, amma abokantakar mu har abada ne

Toh, abokai. Kun banbanta da juna a hanyoyi da yawa ko? Kuma yana rikitar daku wasu lokuta, ko? Abun shine, duk da hayaniyar, abun daya banbanta ku shine ya saka abokantakar ya kara zama na musamman. Baza kuji dadin rayuwa tare ba idan kuka kasance iri daya.

Toh yanzu, bari muyi magana akan kungiyar abokan ku. Mun san cewa akwai abubuwa da halaye da yawa masu ban sha’awa. Kuma tunda muna son yin nishadi a nan, mun hada jerin abubuwa. Mu fara wasan:

Babban Yayan
Itace uwar kungiyar. Tana da hankali. Tana da hikima. Tana da ban mamaki. Tana kula damu kuma wasu lokuta tana kare mu fiye daya kamata. Tana share hawayen masu kuka, kuma tana bawa masu yunwa abinci. Tana tsare kowa. Tana koya muku ku kara kula da bukatun sauran mutane.

Mai kwazon samu
Tana da ilmin sana’a da kudi. Bata jin tsoro kuma tana da buri da kishin kanta. Koda yaushe tana neman hanyoyi da zata samo muku kudi idan baku da. Zata iya magana da kowa. Idan kuna son ku koya yadda za kuyi ajiya da kara samun kudi. Ita ce zaku sama.

Yar gayu
Tabbaci tare da zuciya mai kyau. Za’a iya dogara da ita ta bada dabaru akan komai game da kayan yayi, adon fuska da kuma kula da fata. Zata taimake ku rungume kyawun ku. Tana da hankali kuma tana kare wadanda take kauna.

Mai bada dariya
Mai bada dariya a taro. Wanda kowa ke sauraran labaran ta. Wanda ke saka mutane farin ciki idan kowa na bakin ciki. Tana da karfin hali, amma kuma tana da ban sha’awa. Yin magana da ita nada sauki. Tana nuna muku cewa sau mara kyau basu bace ba idan kuna tare da mutanen kwarai.

Toh gashi nan! Kowa a kungiyar abokan ku na da musamman a nasu hanyar. Saboda haka ku bude zuciyar ku kuyi shagalin banbancin ku. A ta nan, zaku koya zama da mutane da suka banbanta daku.

Yanzu ku gaya mana, wanne ne ya dace daku?

Share your feedback