Ku buge damuwar nan

Ku koya yadda zaku kirkira lokaci domin nishadantarwa

Wasu lokuta zaku ji kamar babu isashshen sa’o’i a rana.

Ya aka son kuyi aikin gida, ku lura da yan uwan ku, ko kuwa ku taimake mahaifiyar ku a shogon ta idan abokan ku na son ku kwashe lokaci tare?

Ku dauke nunfashi. Zamu taimake ku!

Wadannan dabarun zasu taimake ku jurewa idan kuna da damuwa

Ku kirkira wani jerin abubuwan yi
Ku jera dukkan abubuwan da kuke bukatan yi a farkon kowane mako da kowane rana. Ku kunsa aikin gida (kamar gyaran gida), abubuwan nishadi (kamar kwashe lokaci da abokai), da kuma aiki (kamar taimakon mahaifiyar ku a shagon ta).

Ku jera su bisa ga muhimmanci
Menene abu mafi muhimmanci a cikin jerin ku? Menene ke bukatan yi a yau kuma menene zai iya jira har sai mako na gaba?

Ta jerin abubuwan bisa ga muhimmanci, zaku maida hankali akan abubuwa kadan a kowane rana, maimakon tara wa kanku aiki! Wannan zai taimake ku yin aikin ku.
Idan kuna bukatan yin wasu aiki, kuma ku kwashe lokaci da abokan ku. Ku raba shi. Ga misalli, zaku iya yanke shawara fara yin aikin ku sai ku kwashe lokaci da abokan ku anjima.

Ku lura da kanku
Idan kuka lura da kanku, zaku iya magance aikin ku da sauki. Kuyi wani abu wa kanku, koda so daya ne a rana kamar setin minti biyar domin ku huta, ku more wannan abun sha da kuke so a yayin da kuke hira da mahaifiyar ku kafan ku koma yin aikin ku.

Ku fadi gaskiya
Kuyi magana da iyayen ku idan kun gaji da yawan aikin da kuke da. Ku bayyana musu cewa kuna da aiki sosai. Ku tambaye su ko zaku iya musayar aiki da wani dan uwa ku ko kuwa kuyi wani babban aiki a mako na gaba.

Haka ma wa abokai! Idan suna son su kwashe lokaci dukka ranar, amma kun san cewa kuna da aiki mai muhimmanci da zaku yi. Zaku iya kwashe lokaci dasu na lokaci kadan kafan kuje kuyi aikin ku. Ko kuwa zaku iya gwada yin aikin tare abokan ku.

Kuyi kokari kada yin labari a waya ko kuwa yin wasa a maimakon aiki ya kwashe muku hankali.


Ya kuke samun lokaci wa abokan ku? Kuna ganin baku da isashshen lokaci wa kanku? Gaya mana akan sa a wajan sharhi.

Share your feedback