Sha’awa ko kuma kauna: ku san banbancin

Abun mamaki!

Kasancewa balagaggu zai iya zuwa da nishadi. Abubuwan nishadantarwa. Wasu lokuta ma akwai hayaniya. Kamar lokacin da kuke sha’awar wani namiji. Ko kuwa kuna ganin kamar kuna soyayya.

Abubuwar annashuwa na fara aukuwa. Zuciyar ku zai riga bugu da sauri idan kuka gan sa . Kuna tunanin sa kowane lokaci. Kuna san sa a kusa daku. Kuma kuna fatan shima yana jin haka.

Amma abubuwa na iya rikitarwa. Saboda haka, yana taimako ku sani ko sha’awa ne kawai ko kuwa asalin kauna ne. Muje zuwa:

Misali daya
Shekarun Bibi goma sha biyar. Ta shaku da babban yayan ta namiji, wanda ke da aboki mai sunnan Jahda. Duk sanda Jahda ya zo gidan su, Bibi na kasa kallon sa a ido. Yana da tsawo kuma yana da kyau! Ya iya saka kaya. Bibi nason yadda yake magana. Tana son komai akan sa. Harda yadda yake cin abinci. Menene wannan – Sha’awa ne ko kuwa kauna?

Wannan sha’awa ne kawai, Yan Springsters! Yin sha’awar wani wata babban abu ne dake jan hankali. Galibi saboda yadda kamanin mutumin yake ne. Ko kuwa yadda mutumin ke magana ko tafiya.

Irin sha’awar nan baya jimawa. Zaku iya yin sha’awar wani a wannan watar, kuma kuyi sha’awar wani daban a wata na gaba. Al’adar girma ne. Duk mun masaniyar sa.

Misali na biyu
Shekarun Ogo goma sha bakwai. Akwai wani yaro a ungwan su da sunnan Kesiana. Kwanan nan suna yawan kwashe lokaci tare. Idan suna tare tana walwalawa. Ya fahimce ce ta fiye da kowa. Yana sauraran ta kuma yana goyon bayan muradin ta. Baya tunanin ko ita sakarya ce domin tace tana son ta zama yar majalisar dattawa. Ganin Kesiana na kara saka ta farin ciki. Tana kaunar sa sosai. Har ta fara tunanin rayuwar ta na gaba dashi a ciki. Wannan kauna ne?

Eh! Kauna wani shauki ne mai zurfi da dadi da ake nuna wa wani mutum. Soyayya na iya ajiye mutum biyu tare har abada.

Kaunar mutum ba akan kamanin sa bane. Ba karamin abu bane. Kuna son mutum tare da lahanin sa. Kuna son wannan yan kananan abubuwan daya banbanta su da sauran mutane.

Soyayya na zuwa dabam wa kowa. Amma abu daya mai tabbaci shine: Shine abu mafi kyau.

Kamar balagaggu, yana da sauki ku kuskure sha’awa da kauna. Idan kun rikice, ku bude cikin ku, ku fadi wa wani amintaccen babban mutum kamar yar uwar mahaifiyar ku ko kuwa wata babban yayar ku. Eh, bude cikin ku musu ba zai zo da sauki ba. Mai yiwuwa kuji kunya ko kuma ku damu ko zasu tsawata ku. Amma ku tuna, suma sun taba masaniyar wannan kuma suna kaunar ku. Saboda haka, zasu baku shawara mai kyau da zai taimake ku.

Kun taba sha’awar wani ko kuwa kuanar wani? Ya kuka yi? dan Allah ku bamu labari!

Share your feedback