Kada ku yadda murmushi nan ya rude ku

Ku lura da wadannan alamur kashedi

Kiyi tunanin wannan. Kin hadu da wani yaro mai hankali. Kina son sa kuma shima yana son ki. Kowa na fadin cewa kinyi sa’a. Sai kawai, ya canza halin sa.

Kin taba jin wannan? Toh, ba ke kadai bane. Wasu mutane na wayancewa. Saboda haka a soyayya, kina bukatan yin lura da wasu abubuwa da basu dace ba. Ga abubuwan da kike bukatan sani.

Idan yana da kishi: bai dace ba namiji ya ta kishi kowane lokaci. Idan yana yin miki zargin yaudara, wannan alamar ce sarai cewa akwai matsala. Haka kuma idan yana miki zargin kowane kirar waya ko sakon rubutun ki. Ko kuwa ya hana ki yin magana da iyalin ki ko kuwa abokan ki.

Yana gaya miki abun da zaki yi
Idan namiji bai da tabbaci, zai shafi yadda yake bi dake. Zai gaya miki rigar da zaki saka. Ko abun da zaki yi. Ko wanda zaki yi wa magana. Amma kina da izinin bin ra’ayin ki. Saboda haka yakamata ki tsaya tare da wani dake girmama ki da kuma daraja basirar ki. Maimakon wani dake son yayi iko dake.

Baya girmama ki
Yin zagi bai kamata ba. Bai dace namiji yana fadin miku abubuwa masu cin mutunci da mara da’a ba. Bai dace yana miki izgili ba. Dukka wannan na iya lalata miki aunin darajar ki kuma ya saka ki ji kamar baki da daraja. Ki guje mutanen dake saka ki jin bakin ciki.

Zai daina miki Magana
Wasu maza na amfani da shiru kamar makami. Ga misali, bayan kuka yi fada, zai fara share ki. Sai idan kika gwada rabuwa dashi, zai yi barazanar yin wa kansa lahani. Har zai fadi cewa ba zai iya rayuwa ba tare da ke ba. Wannan duk dabaru ne da zai sa ki tsaya dashi. Bai dace ba.

Yana miki ihu
Akwai wata mai himmar aiki da ake kira Maya Angelou. Ta rubuta cewa “Idan mutane suka nuna muku asalin su, ku yarda dasu”. Kalmomi masu hikima. Ku guje kwashe lokaci da maza masu fushi da wuri akan abubuwa da bai kamata ba. Ku guje yan maza dake yin ihu, dake yin muku barazana, ko dake dukan ku, ko kuwa kowane abu da bai dace ba. Babu uzuri wa wadannan mumunar halayyar. Babu soyayyar daya fi asarar kwanciyar hankalin ku ko kuwa aunin darajar ku.

Idan kuna cikin daya daga cikin wadannan al’amurar, dan Allah ku kare shi nan take. Kuma idan namiji na dukkan ku ko yin muku barazana, kada kuyi shiru. Kuyi magana da wani amintaccen babban mutum tun da wuri ko kuwa kuna da yancin kai rahoto wajan yan sanda.

Menene wasu alamur kashedi daya kamata mu lura? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback