Hanyoyi guda biyar da zaku kara samun tabbaci

Ke isasshashiya ce

Wasu lokuta duniya na yin wa mu yan mata girma sosai. Jikin mu na canzawa kuma muna kokarin kara gane kan mu. A lokuta kamar wannan, mai yiwuwa muna shakkan kanmu kuma bamu da aminta.

Amma mu kala gefen haske. Ba koda yaushe bane muke bukatan wani ya tunatar da mu yadda muke da ban mamaki. Zamu iya yin sa da kan mu.

Ku cigaba da karanta siddabarun da zai taimake ku kara tabbaci:

  1. Ku fada da karfi a ji ku: Duk lokacin da baku jin dadi, ku tsaya a gaban madubi sai ku ce “ ina da daraja”, ni isasshiya ce”, ko kuwa “zan iya zama duk abun da nake so.” Ku zabi wanda ya dace da al’amarin ku. Ku cigaba da maimaita kalmomin. Idan kuka cigaba da yin haka, zai nitse cikin ku kuma zai auku.
  2. Ku koya sabobin abubuwa: Ilmi shine karfin iko. Ku karanta littafai da makala na yanar gizo gizo da kuma tambayan tambayoyi akan abubuwa da baku fahimta ba. Ku koya wani kwarewa kamar fenti ko buga ganga. Zaku yi mamakin yadda zai saka ku jin dadi.
  3. Kada ku dame kanku: Yin kuskure al’ada ne. Mu mutane ne. Duk lokacin da kuka yi wani abu da baku alfahari akai, ku tambaye kanku abun da zaku gaya wa wata amintaccen abokiyar ku a wannan al’amarin. Sannan ku maimaita wa kanku wannan abun sai kuyi farin ciki.
  4. Kada ku kwatanta kanku da wasu: Dukkan mu nada musamma a namu hanyar. A lokaci na gaba idan kuna son ku kwatanta kanku da wasu, ku tsaya kuyi tuna cewa ba kamar irin ku. Ko kuwa, ku rubuta jerin abubuwa guda goma da kuke son yi akan kanku sai ku karanta su koda yaushe.
  5. Kuyi setin muradi na kanku: Dukkan mu nada “wani abu” da muke son yi. Ga misali, idan kuna tunanin ajiyan wani iya yawan kudi, zaku iya rage kashe kudin aljuhun akan kayan kwadayi. Maimakon haka, ku ajiye wannan kudin wa wani abu da kuke bukata kamar littafin koyo. Cin nasarar wani muradi babban hanyar ne na karfafa gwiwan ku.

Menene sirrin tabbacin ku? Rarraba da mu a nan kasa.

Share your feedback