Hanyoyi guda huda da zai taimake ku cigaba da abokantaka koda kunyi nesa da juna
Kuyi nishadi da babban abokan ku koda menene
Wasu lokuta babban abokan ku basu zama kusa daku. Saboda haka baza ku riga haduwa sosai ba. Amma ba lallai bane abokantakan ku ya kare. Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya cigaba da tuntubar juna.
Yaya? Zamu taimake ku.
- Hotuna: Zaku iya tura wa juna hotuna. Zai iya zama wani hoto mai bada dariya. Ko kuwa hotuna akan wasu abubuwa da kuke so. Kuma, zaku iya hada ma’ajiyar hotuna cike da abubuwa masu nishadi. Zai zama abu mafi kyau.
- Kungiyar yin tadi: Ku kirkira wani kungiyar yin tadi na musamman wa junan ku kawai. Ku saka shi ya zama naku sarari mai tsira. Ku gaya wa juna komai da komai. Ku tambaya game da ranar junan ku, Ku rarraba damuwar ku da juna, kuma ku bawa juna shawara idan kuna bukatan sa. Kuyi dariya akan abubuwa masu ban dariya. Kuma hanya ne da zaku tsirata kanku. Kafan ku fita, ku gaya wa babban abokan ku inda zaku je kuma da wanda zaku je ku gani. Koda wajan na kusa ne ko da nesa, koda yaushe ku goyo bayan juna.
- Wasannin kan waya: Wasannin kwamfuta wata hanya ne mai kyau da zaku shaku. Wasun su na iya saka mutane biyu ko fiye da haka su hade daga nesa. Wannan yana nufi cewa ke da babban abokiyar ki zaku iya yin wasa a kowane lokaci. Kada ku dauke shi da muhimmanci. Ba akan cin nasara bane. Akan shakuwa ne da kuma yin nishadi.
- Ki da Waka da kuma hoton bidiyo: Ku rarraba wakokin da hotunan bidiyo da kuka fi so da babban abokan ku. Zaku iya yin waka da dariya tare– Koda baku tare. Jeki kuyi tunanin masu ban mamaki. Wannan ne abokantaka na asali.
Yaya kuke yin abokantaka da abokan ku dake wasu wajaje? Gaya mana a wajan sharhi.
Share your feedback