Kuyi nishadi, Ku tsirata kanku

Kwashe lokaci da abokai a hanya mai tsira

Kamar matasa, kwashe lokaci da abokai a lokacin da bamu komai abu ne mai nishadantarwa.

Wasu lokuta, kwashe lokaci da abokai zai saka mu ji kamar munyi girma. Kuma wannan nada ma’ana. Idan muna kara girma, ana kara bamu daman yin abubuwa. Ana barin mu yin abubuwa sosai idan iyayen mu ko masu tsaran lafiyan mu basu nan.

Wa ku, kwashe lokaci zai iya nufi zuwa biki da abokai.

Wa wasu mutane, zai iya nufi zuwa gidan cin abinci ko kuwa zuwa shagon kaya.

Yawancin lokuta, nishadi ne mara lahani. Amma zai iya zama mara tsira. Abubuwa na iya shan karfin ku. Wannan ne yasa iyaye da masu tsaran lafiyar ku ke damuwa akan fitawar ku wasu lokuta. Yakamata mu nuna musu cewa zamu iya yanke shawara mai kyau kuma mu tsirata kanmu.

Zamu iya tsirata kan mu da wadannan dabarun na nan kasa. Musamman idan muna kwashe lokaci da samari.

  • Ku gwada kwashe lokaci tare a cikin kungiya, kamar idan zaku je ku hadu da samari ku tafi da wata abokiyar ku- ku gaya musu su kawo abokan su ma sai ku maida shi wani kungiya mai yin abubuwan nishadi kamar liyafan cin abinci ko kuwa wasan kwallo.
  • Ku guje wajajen zebe. Koda yaushe kuyi kokari ku hadu da abokai a wajan da akwai sauran mutane da zasu gan ku. Wannan zai tabbata cewa kuna da taimako idan wani abu mara kyau ya faru. Wajan kwashe lokacin ku ya zama wajan da zaku samu daman komawa gida a kowane lokaci da sauri idan kuna so.
  • Kada ku sha giya. Wannan bai da kyau. Shan kwayoyi daya saba doka zai saka ku cikin matsala, koda kuna taimakon wani rike su ne zai iya saka ku cikin matsala. Ku guje zama kusa da mutane dake shan kwayoyi ko kuwa wadanda ke son su saka ku sha.
  • Ku gaya wa iyayen ku ko masu tsaran lafiyar ku inda zaku je, wanda zaku je da da kuma lokacin da zaku dawo.
  • Kada ku tafi da baki da baku sani ba. Koda kun hadu dasu da mutane da kuka sani ne.
  • Kada ku bar gida ba tare da waya ko kudi ku kira idan kuna bukata.
  • Kada ku tsaya ku daya da mashaya.
  • Kada ku shiga moto da wani dake shan giya ko kwaya.
  • Kada ku bar abincin ku a bude a cikin jama’a.

Kun taba samun kanku a cikin wani al’amari mara tsira? Ya kuka bi dashi?

Kuna da tambayoyi akan yadda zaku yi nishadi da tsira? Kuyi mana magana a shafin sharhi.

Share your feedback