A taimaka! Anyi wa Facebook dina kutse

Yadda zaku hana sa

Tunanin ku (1)

Sannu Mallamar Fasaha,

Facebook dina na tura mun wasu irin sakonnin rubutu. Ban san meyasa ba. Yana tura mun abubuwa da ban tura wa kaina ba. Abokai na sunce anyi wa shafi na kutse. Menene ma’anar wannan kuma ya zan hana sa?

Nagode, farmaki da kuma bakin ciki

Sannu farmaki da bakin ciki,

Sannu yarinya, ina ji kamar dai anyi wa shafin ki kutse. Wannan yana nufin wani ya shiga shafin ki. Wannan mutumin na wayancewa cewa ke ce. Wannan zai iya faruwa idan kika manta ki fita daga shafin ki. Kin yi mantuwa ki fita bayan kin shiga shafin ki a wani shagon yanar gizo gizo ko kuwa lokacin da kika yi amfani da wayan wani? Ko maiyiyuwa baki fita ba bayan da kika bawa wata abokiyar ki aron wayan ki. Wasu lokuta kwararrun masu yin kutse zasu iya shigan shafuka dayawa da kwarewar su a yin kutse.

Masu yin kutse (koda abokai ne ko baki) na yin wallafa daga shafin ki ba tare da ikon ki ba. Wasu lokuta abokai na yin wannan domin suyi dariya. Koda abun ban dariya ne, yana da muhimmanci ku samu ikon shafin ku nan take!

A shafukan yanar gizo gizo kamar Facebook, zaku iya kai rahoto idan aka kutse shafin ku. Ku bincika shafin “taimako” a kasar shafin ku. Kuma, ku canza lambar sirrin ku, wannan zai iya shawo kan matsalar.

Koda yaushe ku tuna ku fita daga shafin ku, kuma ku kula da lambar sirrin ku. Wadannan dake rubuta lambar sirrin su a littafi, ku tuna kada ku ajiye shi a wajan da za’a iya gani da wuri.

Ku bawa abokan ku shawara kada suyi wasa da shafukan mutane. Baza su so ba idan aka musu haka.

Allah ya bada sa’an shawo kan matsalar kutsen.

Da kauna, Mallamar Fasaha.

Kuna da wani tambaya wa Mallamar Fasaha? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback

Tunanin ku

yayi kyau

March 20, 2022, 8 p.m.