“A lokacin da suke je kasa, zamu je sama”- Michelle Obama
Kalmomi nada karfi. Suna tsayawa dake fiye da kike tunani. Saboda haka, idan wani ya jefa miki magana marasa kyau akan jikin ki, yana shigan kasusuwan ki.
Baki jin dadi kuma kina al’ajabin abun da kika yi da bai kamata ba. Ana kiran wannan kunyata na jiki. Yana faruwa da yan mata kamar mu kowane rana. A lokuta irin wannan, yana taimako kiyi tuna cewa ba laifin ki bane.
Baza ki iya iko da abun da mutane ke fadi miki ba. Abunda zaki iya iko da shine martanin ki. Ga wasu siddabaru da zasu taimake ki.
Kiyi magana kuma ki kare kanki
A lokaci na gaba wani ya kunyata miki jiki, ki bawa mai laifin mamaki da murmushi. Ki gaya musu da natsuwa, cewa kina kaunar kanki a yadda kike. Ki bayana musu dalilin daya sa kalmomin su nada lahani. Ki tunatar dasu su zama masu hankali wa sauran mutane. Kada ki zama kamar su. Banda zage-zage, koda menene.
Kada kiyi kuka
Kiyi kokari kada kiyi ihu ko zubar da hawaye. Wannan abun ne masu laifin suke son kiyi. Kada ki bari su san cewa sun raunata ki. A maimakon haka, ki kirga daga daya zuwa goma a cikin zuciyar ki. Zai taimaka kwantar miki da hankali. Bayan nan, idan kika zabi kiyi magana, kiyi da asalin muryan ki.
Kiyi tafiya
Wasu lokuta yin shiru shine amsa mafi inganci. Dangantaka da halin da kike ciki, mayar da martini bashi da amfani. Yana da kyau ki share kiyi tafiya. Baya nufi cewa kina da rauni. Yana nufi cewa ke babba ce.
Ki kai rahoto
idan wani na miki barazana ko baki tsaro, ki kai rahoton mai laifin wajan wani babba da kika yarda da. Kada kiji tsoron yin magana. Ba wanda keda izinin sa ki jin karami.
dan wani ya kunyata miki jiki, yana fadin abubuwa sosai akan su. Kina da kyau kuma ke na musamman ce. Ki zama kanki kiyi farin ciki. Oh, kuma ki gaya ma wani abu mai dadi yau. Zaki yi mamakin yadda zasu ji dadi.
An taba kunyata miki jiki? Ya kika amsa su? Gaya mana a nan kasa.
Share your feedback