Ku kare kanku
Dabarun tsirata kanku da kuke bukatan sani
Wasu lokuta duniyar bata da tsira.
Mutanen da muke tsammanin mun sani zasu so su raunata mu. Wasu lokuta wani bako zai so ya raunata mu. Wasu lokuta wani da muka sani ne zai saka mu cikin wani abu mai hatsari.
Shiyasa muke bukatan kiyayewa. Ya kamata mu kulla da abubuwan dake faruwa a kusa damu.
Saboda muna son ku tsira a koda yaushe, zamu rarraba wasu dabarun tsira da ku a nan kasa:
- Ku guje wurare masu hatsari. Idan wani ya tambaye ku ku hadu dasu a wani waje da kuke ji kamar bai da tsira kamar wani waje da babu mutane, waje da babu wuta, ko waje dake da shiru. Dan Allah ku guje zuwa irin wajajen nan.
- Kuyi tafiya a fili da abokan ku. Idan kuna jin kamar baku tsira ba a wasu wajaje a wasu lokuta (kamar tafiya zuwa gida da dare), amma idan ya kama dole kuje, ku tambaya wani ya raka ku.
- Koda yaushe ku gaya wa wani inda zaku je da kuma lokacin da zaku dawo. Ta nan, idan abu ya faru, sauran mutane zasu sani kuma su dauke mataki.
- Ku riga gaya wa mutane idan abu ya faru daku ko kuwa abokan ku. Ku tambaya su taimake ku tabbata cewa an shawo kan matsalar kuma kada ya sake faruwa!
- Ku samu wani dabara! Ku nemo wani amintaccen babban mutum da zaku iya samu idan kuna da wani matsala. Zai iya zama Innar ku, ko kawun ku, ko mahaifiyar ku, ko kuwa wata malama. Ku tabbata cewa kun san inda zaku nemo wadannan mutanen ko kuwa yadda zaku tuntube su idan kuna bukatan taimako.
Kun san sauran hanyoyi da zamu iya tsirata kanmu? Ku rarrba damu a sashin sharhi.
Share your feedback