Dabarun fara sabon shekara
Shekarar 2017 yazo ya tafi. Eh abubuwa da yawa sun faru a shekarar daya wuce.
Wasu da kuka yi alfahari da. Wasu kuma da kuka so da kun canza.
Kamar wani daya raunata ku ko kuwa yanke wani shawara da baku yi alfahari da ba.
Gaskiyar shine baza ku iya canza su ba. Amma zaku iya yin wani abu domin ku inganta abubuwa.
Saboda muna son ku samu cigabawa. Ga wasu hanyoyi da zaku iya yin sa:
Ku mata da abun baya
Akwai wani daya gaya muku wani abu daya raunata ku? Kun dauke wani shawara da bai dace ba? Mai yiwuwa kuna kan bakin ciki. Kuna ganin kamar bai dace daya faru daku ba. Kuna ganin baza ku iya mantawa ba.
Eh ya faru. Baza ku iya canzawa. Amma zaku iya canza yadda ya shafe ku. Kuyi kokarin daina tunani akan sa. Ku daina daurawa kanku laifi ko kuwa wani akan abun daya faru. Kuyi tunanin dukkan abubuwa masu kyau da zaku iya yi da kuma cimma buri a wannan shekarar. Ku yi su mataki daya a lokaci.
Ku koya daga masaniyar ku
Kowane masaniya nada darasi. Kuyi tunanin dukkan abubuwa daya faru a shekarar daya wuce. Da mai kyau da mara kyau. Kuna ta shigar matsala a shekarar daya wuce? Mai kuka yi domin ku ceci kanku? Mai kuka koya daga masaniyar ku? Ku tamabaye kanku wadannan tambayoyin. Ku amsa su da gaskiya.
Ku dauke darasi daga wadannan masaniyar. Ta nan zaku koya abun da zaku yi idan kuka same kanku a irin wannan al’amarin a wannan shekarar.
Ku maida hankali a wannan shekarar
Yanzu ne lokacin mai kyau da zaku maida hankali akan abun da kuke so a wannan shekarar.
Ku yanke shawara akan abun da kuke so. Kuna son ku yanke abokantaka da mutane dake raunata ku ne, ko kuna son ku ajiyar kudi, ko kuwa ku daina rike abu a zuciya ku? Ku yanke shawara. Kuyi imani da kanku. Ku aikata.
Ku cigaba da imani cewa abubuwa masu kyau zasu auku a wannan shekarar. Kuyi godiya wa abubuwa da kuka koya a shekarar daya wuce. Ku more shekarar.
Ku karanta makalar mu na kyawu da kuma hikima
Kun taba mantawa da wani abu daya wuce? Gaya mana yadda kuka yi. Kuna da wasu abubuwa da kuke son ku manta daga shekarar 2017? Kuyi mana magana a wajan sharhi.
Share your feedback