Sidabbaru na tsira a watannin karshen shekara

Ki tsirata kanki a karshen shekara

Kungiyar Red Cross na Kasar Naijeriya sun zo makarantar mu yau. Sunyi mana magana akan tsirata kan mu a watannin karshen shekara. Zamu shiga watani na karshen shekara: Satumba, Oktoba, Nuwamba, da kuma Disamba.

A wannan lokacin, Kasuwa na cika. Mutane na shirin Kirsimeti. Akwai kuma taron daurin aure da bidiri. Mutane na tafiya zuwa kauyen su. Akwai karin jerin ababan hawa a kan hanya. kuma lokacin sanyi da iska ne, yana nufin cewa ko ina ya bushe kuma da sanyi.

Ga wasu hanyoyi da ake koya mana yadda zamu tsirata kan mu:

  • Ku kalla hanun daman ku dana hagun ku kafan ku tsallake titi. Ki jira sai wutan hanya ya tsayar da mutane kafan ki tsallake titi.
  • Ku gaya wa iyayen ku ko iyalin ku in da zaku je idan zaku fita daga gida.
  • Ku fita a kungiya. kiyi kokari kada ki fita ke daya.
  • Kuyi kokarin rufe kofofi a gida kuma kada ku bude wa mutanen da baku sani ba.
  • Ku kiyaye idan kuna dafa abinci. Ku kashe kowane abu dake amfani da wutan lantarki ko nau’in sinadarin mai kama da iska idan baku amfani dashi. Kuma ku tabata idan kuka amfani da murhu ku kashe shi da garin kasa bayan an gama amfani dashi.
  • Kada ku je da nesa ko kuwa wajan da baku sani ba domin wasa.
  • Koda yaushe idan kuna rashin lafiya ku gaya wa iyayen ku saboda su lura da ku da wuri.

Yana na muhimmanci mu tsirata kan mu. A lokacin watanin karshen shekara. Kuma a kowane lokaci a cikin shekarar.

Gaya mana wasu sidabbarun tsira a shafin sharhin mu.

Share your feedback