Sakonnin kwamfuta, Zamba, Sankarar kwamfuta! Menene su?

Da kuma yadda zamu kauce su

Tunanin ku (1)

Sannu mallamar fasaha,

Zaki iya mun bayanin menene sankarar kwamfuta? Sankarar kwamfuta daya ne da zamba? Ban tabbata ma’anar su ba. Kawai dai na san cewa dukkan su basu da kyau!

Nagode, Yarinya a jihar Markudi

Sannu Yarinya a jihar Markudi,

Sankarar kwamfuta na iya shigan wayoyin mu ko kwamfutar mu. Yana nan Kamar yadda wani cuta ke shigan jiki. Ba wande yake son sankarar kwamfuta. Zasu iya saka na’urorin mu suyi abubuwan da bamu so. Zai iya tura wasikar lantarki da sunnan mu! Sankarar kwamfuta zasu iya saka na’urar ku su mutu. Wannan zai iya saka mu asarar abubuwa kamar hotuna, wakoki ko kuwa wasani. Ana rarraba sankarar kwamfuta daga waya daya zuwa wani waya (ko kuwa wata kwamfuta zuwa wani kwamfuta). Zamu iya samun wadannan sankarar kwamfuta idan muka bude fayiloli ko shafin yanar gizo gizo. Ku guje buden fayiloli da kuma shafin yanar gizo gizo daga wajan mutanen da baku sani ba. Ku kiyaye idan kuna amfani da na’urar bluetooth domin karben fayiloli. Ku tabbata mutumin dake tura muku baida sankarar kwamfuta a na’urar sa. Ku tambaye su ko suna amfani da manhajar dake kashe sankarar kwamfuta domin kare wayoyin su.

Zamu iya shigar da manhajar kashe sankarar kwamfuta na wayoyi. Ku duba manhajar kashe sankarar kwamfuta a ma’aijyar aikace-aikace na cikin wayar ku. Misalai kamar Google play ko kuwa ma’ajiyar aikace-aikacen Opera idan kuna amfani da mabincikar bayanai na Opera mini.

Idan kuka karbi abu daga wata abokiyar ku da kuke tunanin baza su iya tura muku ba, ku kiyaye. Mai yiwuwa na’urar su ya kama da sankarar kwamfuta. Ku tambaye abokan ku ko su suka tura muku kafan ku bude.

Sankarar kwamfuta zasu iya saka shafukan sada zumunta ko kuwa wasikar lantarki su tura sakonnin “zamba” zuwa abokan ku. Zamba sakonnin rubutu ne da ba’a so da ake tura wa mutane dayawa. Na tabbata cewa bamu son mu tura wa abokan mu irin wadannan sakonnin.

Saboda haka yana da muhimmanci mu tabbata akan wani shafin yanar gizo gizo kafan mu bude sa. Idan wayan ku ko kwamfutar ku ya fara aiki yadda bai kamata ba, ku dauke sa ku kaiwa wani kwararre ( kamar wani a shagon fasaha) da zaran kuka samu dama!

Da kauna, mallamar fasaha.

Kuna da wani tambaya wa mallamar fasaha? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback

Tunanin ku

Fatan Alheri

March 20, 2022, 8:01 p.m.