Ku tsare kanku a al’ummar ku

Dabaru masu inganci wa yan mata

Lafiyar rayuwanku nada muhimmanci.

Kowane rana yan mata na fuskanta al’amurra mara kyau ko kuwa mutane a al’ummar su. Zai iya kasance masu cin zali a makaranta ko kuwa masu tsokana da taba jiki a kasuwa ko cikin motar haya.

Duk da haka ba lallai sai kun tsorata ba.

Amma kuna bukatan koyan yadda zaku tsare kanku. Kuma ga yadda zaku iya yi;

Yin Kimanta
Idan wani ya aikata abu daya hana ku sakewa, ku yanke shawarar abun da zaku ce da kuma fadi. Akwai abubuwa da yawa da zaku iya yi kamar gaya musu su daina, tafiya da sauri, ko kuwa neman taimako daga mutane dake wajen.

Tabbaci
Kuce a’a! Ku fada da karfi, sarai, kuma koda yaushe da wani ke takura muku.

Ku aikata
Idan kuna bukata, kada kuji tsoron aikatawa domin cin zarafin ko takurar ya daina. Daukan mataki zai iya zama kowane abu daga yin gudu. Fusakanta wani a cikin jama’a zai fi tsirata ku. Idan kuna nan ku kadai kuyi tunanin hanyoyi da zaku kauce.

Kaucewa
Kuyi kokari ku guje mutane dake hana ku sakewa ko kuwa dake kama da masu barazana. Kuma, ku guje wasu wajaje da kuka san cewa na da yiwuwar samun kasada. Gujen wajajen nan ko kuwa al’amurrar nan hanya ne mai kyau da zaku tsare kanku. Kuma zai taimake ku gujen tafiya ku daya da dare.

Ku tsara wani dabara
Ku nema wani amintaccen babba da zaku iya samuwa idan kuna da matsala. Ku tabbata kun san inda zaku samu wadannan mutanen ko kuwa yadda zaku tuntuba su. Kuyi hulda da abokan ku akan yadda zaku nema mutane da zaku iya yarda da ko kuwa wanda zaku iya kai wa rahoto.

Lafiyar ku ne abun muhimmanci a wajan mu.

Akwai wasu hanyoyi da kuke tunani zaku iya tsare kanku a al’ummar ku? Ku rarraba damu a sashin sharhi.

Share your feedback