Muyi shagalin babban kasar mu
Gobe Najeriya tayi shekaru hamsin da bakwai. Shekaru hamsin da bakwai tun da muka karbi yancin mu daga Britaniya.
Ya kasance doguwar tafiya mai wahala da jin dadi.
Yawancin lokuta muna tunani “wahalar”.
Meyasa bamu da hanyoyi masu kyau?
Meyasa bamu da tsayayyen wuta?
Meyasa bamu da makarantun jama’u masu kyau kamar yadda muke ji a can kasar waje?
Amma idan muna son mu maida Najeriya ta zama kasar da muke so, dole mu imani cewa muna da karfin da zamu canza ta.
Zamu iya samun makarantu masu kyau, hanyoyi masu kyau da kuma asibitoci.
Zamu iya samun manyan shugabanni mafi inganci. Zamu iya ingantar da rayuwar talakawa.
Gaskiyar shine, kafan ya faru dole dukkan mu mu aikata wani matsayi.
Kada ku zauna kuyi mafarki kawai. Yan Springster! Ga wasu hanyoyi da zaku fara….
Zamu iya farawa ta saka al’ummar mu waje mafi inganci. Wannan zai gudanar da wani ungwa mafi inganci. Sa’an nan wannan zai iya gudanar da wani karamar ukuma, ko jiha, da kuma kasa. Gaskiya yana farawa daku ne!
Ku sa kai ku taimaka a wani gidan marayu, ko asibiti ko kuwa cibiyar al’umma. Wannan baya taimakan mutane kawai, kuma zaku samu alfanu daga sa kai. Zaku samu ku koya wani sabon kwarewa kuma ku hadu da sabobin mutane. Duk wannan zai taimake ku a rayuwar ku na gaba.
Kuyi magana akan abubuwa masu kyau a Najeriya. Iyayen ku, Masu tsaran ku, yayyi da kuma takardun tahiri na yawan magana akan yadda abubuwa ke da kyau a da. Ku kokarin koyan dalilin daya sa suka canza. Ta nan, zaku kara sanin akan abun da zamu iya yi domin mu kara inganci fiye da da.
Ku naima hanyoyi da zaku zama shugaban ajin ku ko na makarantan ku. Ko kuwa zaku iya fara jagoranta wani kungiya a ungwan ku kamar yin waka ko kuwa kungiyar ajiya.
Tare, zamu iya kirkira Najeriyar zuciyar mu. Ku tuna cewa yana farawa ta saka al’ummar ya zama mafi inganci.
Ku yi wa Najeriya fatar barka da ranar haihuwa a shafin sharhi. Gaya mana akan Najeriyar zuciyar k.
Share your feedback