Ranar yar mace na kasa da kasa
Ke ‘yar mace ce kuma da shekaru goma sha takwas ko kuwa kasa da haka?
Yau, rana goma sha daya a wata na goma a shekara.
A shekara dubu biyu da goma sha biyu, majalisar dinkin duniya (wata kungiya dake kawo kasashe tare domin zaman lafiya da ci gaba) ya fara a wannan ranar domin muyi magana akan yan mata a duniya.
Akwai yan mata guda biliyan daya da dari daya a duniya, wannan babban lamba ne!
Yakamata dukkan mu mu samu muje makarantu masu kyau, muyi dogon rayuwa kuma mu ci nasara a burin mu.
Kuma ya kamata mu samu muyi aure mu samu yara a lokacin da muka shirya wa wannan bangaren rayuwa.
Yau, kungiyoyi da yawa na magana akan yadda zasu tabbata cewa yan mata sun samu yanci musamman mu da muke wajajen da akwai yaki da sauran matsaloli.
Muyi taimako ta yin wa abokan mu da iyalan mu magana akan yadda zamu albarkace rayuwar yan mata a al’ummar mu.
Kuma muyi farin ciki yau, mu dauke hotuna kuma mu fada dalilin da yasa muke alfaharin Kasancewa yan mata.
Barka da ranar ‘yar mace!
Gaya mana abun da kike fatan wa yan mata a gaba dayan duniya a wajan sharhi.
Share your feedback