Ki Na Son Kawaye?

To Ki Zama Kawar Kirki Ga Saura.

Tunanin ku (2)

Ƙawaye na saka rayuwa ta zama mai ban dadi da annashuwa da dariya kuma ta rage nauyin damuwarki. Akwai miliyoyin hanyoyi da za ki zama ƙawar kirki! Yawan kawayen da kike da shi ke da mahimmanci ba. Abin da ke da mahimmanci shi ne ki zama kawar kirki ga mutanen da kika damu da su.

Ga wasu dabaru:

Babbar doka ita ce yi tunani dangane da abin da ki ke nema da bukata daga ƙawa – kuma ki aikata hakan zuwa ƙawarki.

Ki saurari ƙawayenki kuma ki girmama ra’ayoyin saura – ko da ra’ayoyinsu sun saɓa da na ki.

Ki so kawayen ki yadda suke. kawayen kirki ba sa sukan kawayen ko suyi kokarin canja su. Ki daraja kawayen ki domin yadda su ke kuma ki bi da su ta yadda zaki so kema abi da ke.

Ki zama mai fahimta kuma mai yafiya. Ki saka kanki a matsayin ƙawarki’ – mu duka muna yin kuskure.

Ki zama mai amana. Wannan na nufin yin abinda ki ka ce za ki yi kuma kada ki yiwa ƙawayenki yankan baya. Kada ki bayyana sirrin da ƙawayenki suka bayyana miki, har sai in sun shiga cikin wani haɗari. Idan su na cikin haɗari kuma su na bukatar taimako, nemo wani babban mutum da ki ka amince da shi domin yin magana da shi.

Share your feedback

Tunanin ku

Na ydda d kawayena

March 20, 2022, 8:04 p.m.

kawaye

March 20, 2022, 7:59 p.m.