Ga Wasu Shawarwari Nan
Jarraba sababbin abubuwa idan kin sami dama. Za ki iya samun wata baiwa wadda ba ki san kina da ita ba!
Ki Ƙarfafa wa kanki gwiwa ta yin tunani mai kyau akan yunani marar kyau. Misali, ki faɗawa kanki, ‘ ni ina da ƙarfin gwiwa, ‘ni kyakkyawa ce ’ ko ‘ zan iya yin wannan. ’ Nemi ƙawaye masu ba da shawara waɗan da zasu tallafa miki domin haɓaka baiwarki. Ƙawaye na iya ƙarfafa miki gwiwa domin ci gaba da ƙoƙartawa ko da kin gaza. Kuma suna iya ganewa lokacin da ki ke murna kuma su yi murna tare da ke. Ki dinga zama da ƙawayen kirki waɗanda ke ƙarfafa miki gwiwa.
Duk wanda ya fara balaga ya na jin wani abu a cikin zuciyarsa. Idan ki ka ji abin cikin zuciyarki ya lulluɓeki, zai taimaka idan ki ka ja numfashi, domin yin wani abu kamar rawa ko ki yi tafiya (idan akwai tsaro), ko ki sami mutumin da ki ka yarda da shi domin hira ko magana da shi.
Share your feedback