Zama mai yancin kai- Sashi na daya

Yana farawa da ku!

Tunanin ku (1)

Sunana Lara, shekaru na goma sha bakwai. A shekarar daya wuce, ina zuwa makaranta. Bana taba rasa abincin ci. Kayan sakawa. Abun da nake so kawai a rayuwa shine na zama mai yancin kai. Kuma, bana son nayi tunani ko wani abu zai iya hana ni.

Sai, mahaifina yayi asarar aikin sa. Abubuwa suka bace. Sanda na bar makaranta saboda mun kasa biyan kudin makaranta.

Barin makaranta ya kasance da wuya. Saboda yana nufin cewa muradi na na zama mai yancin kai zai mutu. Naji kamar bazan iya cimma burina idan bani da ilmi.

Amma wata rana sai tunani na ya canza bayan na karanta wani labari a shafin Springster. Sunann labarin “ Zama naki shugaban”. Shine abun da nake bukatan karantawa a wannan lokacin.

Ta labarin nan, na koya cewa zan iya fara nawa kasuwancin kuma na zama mai yancin kai. Ilmi ba shi kadai bane hanyar cimma buri.

Kuma na koya cewa mataki na farko na zama mai yancin kai shine tabbaci da imani da kai na da kuma ikon cimma buri na.

Na san wasu lokuta yana da wuya a samu tabbaci musamman idan komai bai zuwa daidai. Amma a maimakon maida hankali a abubuwa mara kyau, zaku iya yin wadannan abubuwan biyu.

Ku yi tunani masu kyau <br Masu ilmin kimiyya sun ce saba’in daga cikin darin tunanin mu basu da kyau. Kun san wannan? Kuma kaka na tace “Tunani mara kyau ba zai bada rayuwa mai kyau ba”. Kuma ta fadi gaskiya. Idan kuna son ku kasance masu yancin kai dole ku yada tunani mara kyau domin ku rungume masu kyau. Dole ku koya ganin haske a cikin kowane duhu.

Ku san kwarewar ku da gwanintar ku
Da nake makaranta, na iya lissafi sosai. Ina tunanin zan iya yin amfani da wannan kwarewar domin na sarrafa wani sana’a.
Yana da muhimmanci ku san abun da kuka iya yi sosai. Sai ku maida hankali a kan shi. A ta nan zaku kara samun tabbaci a kanku.

Ku tuna, tunani ku zai iya tasirin shaukin ku. Shaukin ku zasu yi tasirin shawarar da kuka yanke da kuma ayyukan ku.

Kafan ku zama masu yancin kai, sai kun amince cewa zai iya yiwuwa ku cimma burin ku. Kuma kun san mene yan mata? Yana yiwuwa.

A dan kwanaki na gaba, zan rarraba karin bayanai akan tafiya na zuwa yancin kai. Saboda haka, ku saurara wannan shafin domin. “Zaman mallama mai yancin kai- shafi na biyu”.

Kuna ganin samun ilmi ne kadai hanyar cin nasara a rayuwa? Ku rarraba tunanin ku da mu a sashin sharhi.

Share your feedback

Tunanin ku

Lailai kinyi kokari Allah bada sa'a

March 20, 2022, 7:54 p.m.