Zaki iya barin sa
Sannu Babban yaya,
Ina cikin wani babban matsala!!! Yi hakuri na tada miku hankali, amma ina bukatan taimakon ki. Kin gani, yana da hankali. Kuma yana nan haka da kowa, ba ni kadai ba kawai. Abokai na sun ce nayi sa’ar samun sa.
Ba zan yi karya ba, ban tabbata da yadda nake ji ba sanda na yarda na fita dashi. Ina son sa, amma ba sosai ba. Na zata kaunar zai karu. Dukka abokai na nada samari, kuma na gaji da ji kamar an bar ni a baya. Amma bayan shekara daya, bana son sa kuma! Ba wai munyi fada bane. Ko ya mun wani abu da bai dace ba. Kawai na tashi wani rana naji zuciya na ya canza gaba daya!
A da ina son dariyar sa. Amma yanzu idan yayi dariya, ina son na guje shi. Bana jin dadin zama kusa dashi kuma kamar da. Wasu lokuta ina son na zauna ni daya. Amma baya bari na.
Ina bakin ciki! Ina son na rabu dashi! Amma ina jin wani iri saboda laifi na ne. Da ban yarda nayi soyayya dashi ba tun da fari. Bana son na bata masa zuciya, kuma bana son abokai na suga kamar nayi hauka.
Mai zan yi Babban yaya? Dan Allah ki taimaka!!!
Nagode,
Wunmi-a-cikin-wahala
Sannu Wunmi-a-ciki-wahala,
Naji dadin da kika rarraba labarin ki da ni. Ba hauka kike yi ba. Kina cikin fargaba ne kawai, kuma ba komai bane idan kika aikata abu haka a cikin irin wannan al’amarin.
Naga kamar kin canza yanayin ki a shekara daya da ya wuce. Mai yiwuwa a lokacin nan, kin matsu ki fara soyayya saboda abokan ki. Mai yiwuwa kin canza ra’ayin ki. Shiyasa zaki so ki kwashe lokaci ke daya domin ki kara sanin kanki.
Wannan al’ada ce da yan mata shekarun ki. A wanann lokacin a rayuwar ki, kina kara koyar abubuwa akan ki kowane rana. Mai yiwuwa baza ki ji dadin yin abubuwan da kike yi a watani da suka wuce ba. Ko kuwa ki cigaba da rayuwar kamar yadda kika saba. Zaki iya canza ra’ayin ki akan kowane mutum ko abu. Kada ki dame kanki, kin ji?
Idan kika daina son wani, bai kamata ki cigaba da zama dasu ba. Saboda haka kada ki cigaba da zama da saurayin ki dan kina tausayin sa. Bai kamata ku tilatsa kanku a soyayya ba. Dukkan ku biyu na cancanta rayuwa mafi kyau.
,br>
Ki zaunar da saurayin ki kuyi magana. Ki gaya masa cewa kin canza ra’yin ki. Kuma zai fi idan kowa ya kama hnayar gaban sa. Kada kiyi fargaba. Ki tabbata kin hadu dashi a fili a waje, kiyi masa magana da hankali, amma kada kiji tsoron gaya masa yadda kike ji.
Kiyi kokari kada kiyi tunanin abun da abokan ki zasu fadi. Kina rayuwar ki wa kanki ne, ba wa wani ba. Kuma, idan su abokan arziki ne, zasu girmama ra’ayin ki.
Ki tuna, ba komai idan kika yanke shawara cewa baza kiyi soyayya ba sai kin shirya. Saboda haka, ki dauka lokacin ki. Kuma kiyi nishadi.
Ina fatan wannan ya taimaka. Ki gaya mana yadda ya kasance.
Da kauna,
Babban yaya
Akwai wani na musamman a rayuwar ku? Zuciyar ku ya canza akan su? Gaya mana a sashin sharhi.
Share your feedback