Yin kafiya nada muhimmanci

…..ya taimake ni fara nawa kasuwancin

Ya fara a falon mu.

Abokai na, yan uwa na, da ni na zama na magana akan yadda zamu yi kudi. Mu zama kamar Dangote ko kuwa wadannan mawakin masu kudi. Dukkan mu na yin wannan.

Amma wannan lokacin ya bambanta, abokin wa na ya gaya mun wani abu daya canza mun rayuwa.

Yace “Zainab, kina son takalma, toh ki fara sana’ar takalma mana?

Da farko nayi dariya na gaya wa kai na yara daga gidan masu kudi ne kawai zasu iya fara irin wannnan sana’ar.

Amma sai na kara tunani. Ba wanda aka haifa da kudi, kowa na farawa daga wani waje ne.

Kwatsam kawai, na shiga yin bincike. Naje yanar gizo gizo na fara neman mutane dake sana’ar takalma. Na fara bin su har wasun su ma suka bi ni a shafin sada zumunta.

Na fara tambayen su akan abubuwa - yadda suka fara, yadda suke tafiyad da kasuwancin su da kuma sauran abubuwa. Na koya abubuwa sosai.

Na yanke shawara akan sunan kasuwanci na kuma na fara yin zane zanen takalma. Sai na naima wani daya iya mai gyaran takalma a al’ummar mu da zai iya taimako na yin takalman.

Sai na nema taimako daga abokai na da iyali na. Na yi ajiyar wasu kudade amma ina bukatan kari. Na rubuta dukka dabaru na, sai nayi amfani dashi na bayyana wa abokai na da iyali abun da nake son nayi da kudin.

Ban samu dukka kudin da nake bukata ba amma sai na fara da abun dana samu. A maimakon yin takalma goma kamar yadda na tsara zanyi, sai na yi uku kawai.

Kuma mutane a ungwar mu suka siya dukka, sun ce takalma ya bambanta dana kowa.

Nayi murna sosai ranar! An kara karfafa gwiwa na na cigaba kuma nayi kokari. Mai yin mun takalmar ya kasa yin da yawa a lokaci daya sai bayan watani kadan, na yanke shawara na fara shigar da takalma daga kasan waje.

Nayi dan bincike kuma na tambaye abokai na na yanar gizo gizo su taimaka su hada ni da wasu mutane. A karshe, na yanke shawara na siyo takalma daga wajan wata mata a kasar China. A haka na fara kasuwancin kasa da kasa na siyan takalma da sayarwa.

Takalman suka shiga Naijeriya bayan sati biyu, ina ta alfahari dana je na karbe su. Suna da kyau kamar na hoto. Nayi muran dana dauke lokaci na nema amintacciyar mai saidawa.

Dole na shawo kan matsaloli da yawa - tsoron siya daga mutumin da bai dace ba, tsoron cewa baza a siya takalma na ba, tsoron asarar kudi na. A gaskiya, wasu dana saida da farko ban saka riba na ba. Amma na koya daga kuskure na da sauri, ina tambaya kowane lokaci kuma ina da kafiyar cimma burina.

Ina kan yin aiki domin kara inganta sana’a na kuma wasu lokuta ina kuskure. Amma abun muhimmanci shine ina nan da burina a rai na. Ina son na kara girmar da kasuwanci na har sai fadin duniya sun ji akan takalma na. Idan na san burina, ina maida hankali akan sa.

Ku fa? Kuna kokarin yin wani abu da kuke ganin ke da wuya? Ku rarraba da mu, mai yiwuwa mu iya taimakon ku da shawara masu kyau ko kuwa amsa wa tambayoyin ku.

Share your feedback