Nakasasshiya amma baza a iya tsaidani ba

Yadda Abibat ta zama kwararriyar mai daukar hoto

Suna na Abibat kuma shekaru na goma sha shida.

Da nake shekaru biyar nayi asarar kafafu na, wannan ya saka ni kasa tafiya. Mahaifiyata tace cutar shan inna ne ya sanadin sa.

Yanzu ina bukatan keken hannu ko sanda domin na motsa jiki.

Wannan bai bani daman tsoma hanu a ayyuka ba.

Wata rana da nake kallon talabijin, naga nakasasshun mutane na yin wasannin motsa jiki. Ana kiran sa wasannin motsa jiki na nakasasshu. Ban taba sanin cewa akwai gasa haka ba.

Sai nayi tunani, idan zasu iya yi, nima zan iya yin komai.

Sai na yanke shawara nan take cewa nima zan iya koyar wani aikace-aikace. Bazan bari tawaya na ya hana ni ba.

Nayi tunanin abun da zan iya koya. Sai na zabi daukan hoto. Ina son hotuna.

Nayi wa dan uwar mahaifina dake daukan hoto magana, na tambaye shi ya koya mun. Ya yarda.

Ya dauke ni kusan wata daya na koya. Har ya ara mun na’urar dauan hoton sa domin nayi gwaji.

Na fara da daukan yan uwa na hotuna da na’urar daukan hoton.

Hotuna na na farko basu kai nashi kyau ba, amma ban sa wannan ya hana ni ba.

Har wasu mutane a ungwan mu suna mun dariya. Suna tambaya ya aka yi mace da bata tafiya na daukan hoto. Wannan ya saka ni bakin ciki. Nayi tunanin dainawa. Dan uwan mahaifina yace kada na bari su saka ni canza ra’ayi na.

Yace na tambaye mutanen dake mun dariya su tsaya nayi musu hoto. Kuma suka yarda. Suka fara rokona na dauke su hotuna. Wasu lokuta ma suna bani kudi.

Yanzu ina taimakon dan uwan mahaifina a wurin daukan hoton sa.

Wata rana ina fatan zan samu nawa wajan daukan hoto da na’urar daukan hoto na. Zan zama sananniya kamar T.Y Bello.

Bazan bari wannan tawayar ya hana ni zama mai daraja ba.

Sannu Springster, kuna nan kamar Abibat kuma mutane sun gaya muku cewa baza ku iya cimma burin ku ba. Wannan karya ne. Mutane da kowane irin tawaya zasu iya zama likitoci, ko injiniyoyi, ko mawaki, ko masu zane-zane da sauran abubuwa da yawa.

Kun taba fuskance wani inkari kamar Abibat? Gaya mana burin ku da kuma abun da kuke yi domin ku ci nasara.

Share your feedback