Kara sanin mahaifina

Diyar babban ta har abada

Sannu Springsters!

Suna na Nyela kuma ina farin cikin saduwa da ku! Ban taba kusa da mahaifina ba. Amma kwanan nan, abubuwa sun canza tsakanin mu. Kuna son ku san cikakken labarin? Gashin nan:

Mahaifiyata tayi tafiya zuwa Ibadan domin aiki. Saboda haka ni da yan uwa na maza muka tsaya a gida da mahaifin mu. Da farko, ina kunya kuma ina kasa natsuwa akusa da mahaifina. Ban san abun fadi ba. Na saba da mahaifiyata.

Yan uwa na basu damu ba. Koda yaushe suna wasa da mahaifin mu. Suna wasannin buga kati da sauran abubuwa masu nishadi. Duk sanda suka ce na hade dasu, ina ki. Amma duk da haka ina ji kamar an bar ni a baya.

Sai a ranar Sati, mahaifi na ya kai ni yawo a keke. Mu biyu kawai. Mun zagaye ungwan mu. Na gaya masa akan babban abokiyata, Isioma. Yayi farin cikin jin cewa ina kaunar darasin lissafai. Yace da yake makaranta ana kiran sa “Da Gee”. Nayi dariya sosai.

Bayan da muka koma gida, ya dafa mana shinkafa. Yayi dadi sosai. Abun ya bani mamaki. Ashe mahaifina ya iya abinci! Bayan abincin rana, ya saka mana wakokin 2face da Hadiza Gabon. Munyi gasar ruwa. Ban taba sani cewa mahaifina ya iya rawa ba. Yace da yake shekaru na, yayi sha’awar zama kwararren mai ruwa.

A rana mai zuwa, muka buga ludo. Ya nuna mun wasu siddabaru da zai taimake ni ki cin nasara. Na gwada su kuma suka mun aiki. Nayi murna sosai! Ya gaya mun cewa cin nasara akan dabara ne (wato yin tsare-tsare na nan gaba), ba tilasta ba.

Anjima, ya kai mu cibiyar matasa. Bai zauna da sauran iyaye ba. Yayi wasanni damu, ya gabatar da kansa wa abokan mu. Suka ce munyi nasarar samun mahaifiya mai gagarumi.

Da mahaifiyar mu ta dawo, na gaya mata komai. Take ta murmushi. Tace mahaifin mu ne ya kawo dabarar. Kun ga, ya lura cewa bamu kusa ba. Sai ya yanke shawarar canza abubuwa. Abun ya taba mun zuciya.

Shikenan abokai! Ina fatan na wahayi ku kwashe lokaci da mahaifin ku ko kuwa wani dake tsaran lafiyar ku. Kamar ni, zaku yi mamakin abubuwar da zaku gano: Mahaifu ma mutane ne. Kuma sun hadu! Sai anjima!

Ya kuma zamu iya kara sanin yan dangin mu maza da suka girme mu? Rarraba ra’ayin ku a wajan sharhi.

Share your feedback