Wa yafi yanci?
A ranar farko na makaranta, wani yaro ya taba wa Tomiwa duduwa. Kuma ba ranar daya fara na kenan. Amma lokaci ya kai da zata ce “Ya isa!” wa samari da basu girmama ta ko sauran yan mata a makaranta. Wannan lokacin baza ta kyale su ba. Lokacin ya kai da za’a kawo karshen wannan ayyukan- kuma tayi.
Ga yadda tayi:
Ku san Yancin ku
Tomiwa ta san halayyar su bai dace ba. Yan mata nada yancin da za’a girmama jikin su. Kuma yan mata nada yancin jin dadin ilmi kamar samari. Ta san duka wannan shiyasa taki ta amince da wannan martani dake cewa “samari zasu yi duk abun da suke so”.
Ku ilmantar da al’umma kuma ku kai rahoto
Tomiwa ta tara labarai na yan mata a ajin ta da makarantar. Tayi mamakin yadda yan mata da yawa suka rarraba labaran su. Suma suna fushin cewa ba’a horar da samarin. Ta rarraba wadannan labaran da iyayen ta, suma suka rarraba da sauran iyaye har sanda ya kai kunnuwar hukumar makarantar.
Kuyi magana
Mutane zasu gaya muku kada kuyi magana. Idan abu ko wani ya hana ku sakewa, ko basu girmama yanci ku ba, kuyi magana. Abun daya dace kenan. Kamar Tomiwa, zaku iya yin magana da mutane da kuka yarda da. Yar uwar ku, iyayen ku, mallamar ku ko kuwa abokan ku. Ku saurare mut
Ku mallake karfin ku
Ku san cewa kuna da ikon canza abubuwa. Kada ku taba barin mutane su saka tunanin cewa kasancewa mace yayi kasa da kasancewa namiji. Kowane rana, a gaba dayan duniya, mata da yan mata na kara inganta al’ummar su. Har yan kananan ayyukan karfin zuciya, na iya yin karfin tasiri.
Ta yin magana da kuma rarraba labaran sauran yan mata, Tomiwa ta iya saka makarantar ta su kafa dokar horar da samari dake cin zalin yan mata.
A nan gaba idan wani ya sake fadin muku cewa “ samari zasu yi duk abun da suke so”, ku san cewa kuna da yancin daga muryan ku. Ba sai kunyi sa kamar Tomiwa ba. Amma zaku iya kula da sauran yan mata dake rarraba labaran su daku. Akwai karfin zuciya a hadin kai kuma tare, muryoyin ku zai iya yin tasiri.
Kun taba samun kanku a al’amarin Tomiwa? Ku rarraba masaniyar ku damu a sashin sharhi.
Share your feedback