Yadda zaku zama masu adon fuska

Abokiyata ta taimake ni yin imani da kai na

SANARWA: ANA BUKATAN MAI ADON FUSKAN WA WASAN KWAIKWAYO NA AL’UMMA. KU NEMA YANZU!

Nayi fargaba dana karanta sanarwar. Ina son na nema, amma ina tsoro. Ina son yin zane, kuma daman na iya zanen hotuna. Amma zan iya yin zanen ado a fuskan mutum? Ban tsammanin ba.

Na yanke shawara na share zancen kenan sai abokiyata Lola- jarumar wasan kwaikwayon- ta same ni. “Tunanin me kike yi, Deborah?”" ta tambaye ni. “Ba komai” na amsa ta.

“Na san wannan fuskan,” Lola tace. “Me ke damun ki”

“Em...ina al’ajabi ne ko zan iya yin wa mutunan adon fuska na wasan kwaikwayon”.

“Eh mana zaki iya!”* Lola ta amsa. Kamar wannan bai isa ba sai ta kara fadin cewa ni ce mutum mafi fasaha da natsuwa da ta sani. Tace na zo na ganta washegari domin nayi gwaji da sauran masu wasan kwaikwayon. Bani da tabbaci da dukka wannan. Amma Lola tayi imani da ni sosai har sanda nima na fara imani da kai na. Sai na yarda nayi.

Dana kama hanyar gida, na fara ji dama ban yarda nayi ba. Na yanke shawara na canza ra’ayi na, na bawa Lola hakuri. Duk da haka, dana kai wajan a ranar, masu wasan kwaikwayon na jira na. Suka mun marabta da fara’a. Basu da zuciyar canza ra’ayin su kuma.

Kowane daga cikin su suka nuna mun irin adon fuska da suke so. Bayan nan, na fara bugun fuskar su. Kada kuji tsoro fa. A masana’antar adon fuska, bugun fuska na nufin cewa ana shafa kayan adon fuskar da kyau. Ba wai ana nufin ana duka da gaske bane.

A ranar, na juya daya daga cikin mazan zuwa mace mai shekaru goma sha biyar. Sai na juya kamanin Lola ya koma kamar na wata sarauniya. Munyi nishadi sosai.

Da darektan wasan ta ga aiki na, tayi mamaki sosai har sai ta bani aikin nan take. Nayi murna sosai. Nayi ta wa Lola godiya har sanda ta roke ni na daina. Gaskiyar shine, da ba don ita ba, da ban iya yi ba.

Nayi adon fuskan wasan kuma na samu yabo sosai. Mutane suka fara biya na nayi musu adon fuska na zuwa biki da sauran wajaje. Yanzu ina hanyar zama kwarerriya. Ina son na samu nasara kamar sanannun masu adon fuska kamar Mamza Beauty da kuma Tara. Kuma zan cigaba da yin aiki sosai domin na ci nasara.


Kuna tsoron fara wani abu da kuke son kuyi? Zamu iya taimakon ku! Muyi magana a sashin sharhin.

Share your feedback