Yadda na fara sana’an yin cake.

Labarin Esther na ishara

Hutun nan daya wuce, Iyaye na suka aike ni gidan ‘yar Uwan mahaifiya ta, Aunty Tope. Ban so naje. Ina son na kwashe lokaci da abokai na. A ranar farko na da Aunty Tope, ban yi murmushi ba da ta mun murmushi. Ina ta marmarin gida.

Da safe, na tashi da kamshin gasashen cake. Na naima kamshin zuwa madafa. Aunty Tope na yanke cake. Na gaishe ta nayi tayi na taimake ta. Amma tace na zauna naci yanki daya.

Dana saka a baki, na rufe idanuwa saboda dadin. Cake din da dadi sosai. Na bude ido na naga Aunty Tope na kallo na. Wannan lokacin, da ta mun murmushi, nima sai na maida mata murmushin.

Aunty Tope ta gaya mun akan cakes daban daban, akan sinadaran abinci, da kuma launi. Ta koya mun yadda zan auna abubuwan da ake hada abinci da kuma yadda zan gauraya su da kyau. Bayan wasu lokuta, nayi cake da kai na. Aunty Tope tace nayi kokari. *

Kafan na bar gidan Aunty Tope, ta bani wasu kayan aikin cake. Ta karfafa gwiwa na cewa na cigaba da yin cake, na dauke shawarar ta ina yin cake a lokacin da bana komai.

Da abokai na suka dandana cake dina, basu yarda cewa ni na yi ba. Na gaya musu zan kara yin musu wani idan zasu biya ni naira dari wa kowane yanka. Sai suka bani mamaki, suka yarda. Na kara yin wani cake sai suka siya dukka. Suka rarraba da sauran mutane da suka fara gaya mun na musu.

A yau ina cajin naira dari biyu da hamsin wa kowane yanka. Ina yin cake na ranar haihuwa. Iyaye na suka taimake ni bude wani asusun ajiye kudi na waya. Ina amfani dashi saboda na ajiyen kudi da zanje makarantan koyan cake.*

Wannan ziyarar zuwa gidan Aunty Tope ya canza mun rayuwa. Na fara sana’a kuma na koya kwarewa

Share your feedback