Yadda Sophie ta gyara rayuwar ta

Ba wanda keda izinin saka ku jin bakin ciki

11th Augusta

Sannu Mujalla,
Kasan mene??? Na hadu da wani yaro! Sunan sa Emeka! Yana da komai da nake so– tsayi, kyau, kuma ya bani shekaru uku! Yana saurara na idan ina magana. Yana saka ni dariya. Kuma yana so na da gaske. Ina farin ciki sosai! Abokai na na mun wasa dan bani da saurayi. Wake yin dariya yanzu? Da zan so ku hadu. Ko yaya dai, zan hadu dashi gobe. Bara naje na dauka rigar da zan saka. Sai anjima.

Satumba 21st

Sannu Mujalla,
Mun dade da magana! Ina kwashe lokaci da Emeka. Bani da lokacin ganin abokai na ma. Yana kishi duk sanda nake nan dasu. Ina ganin domin yana kauna na sosai ne. Amma wasu abubuwan da yake yi, ban tabbata ba.

Wani lokaci, naje gidan sa. Yace nayi wa shi da abokan sa abinci. Nace masa bazan iya ba. Yace dole sai nayi. Yace girkin abinci aikin mata ne. Abun ya bani haushi, na bar gidan. Yaki ya bani hakuri.

Oktoba 3rd

Sannu Mujalla,
Ya sake faruwa! A mako daya wuce, naje na siyo suya da Emeka. Nace zan biya kudin. Haka kawai yayi fushi. Yace wani namiji ya bani kudin. Na gaya masa daga sana’ar siyar da silifas dina ne. Yace yan matan arziki basu “samun kudi”.

Bayan dana kai gida, nake ta tura masa sakon rubutu har cikin dare. Bai amsa ba. A karshe dana gan sa, yace ya batar da wayan sa. Kawai, sai naji wayar sa na bugu!

Na gaya wa abokiya ta komai. Abun ya bata haushi! Ta gaya mun na bar shi. Tace na cancanci fiye da haka. Amma ina son na kara bashi dama. Mai yiwuwa ya canza.

Nuwamba 4th

Sannu Mujalla,
Na aikata! Na rabu da Emeka! Na kasa cigabawa. Na gaya masa bana son sa a rayuwa ta kuma. Na gaya masa cewa ina cancancin wani dake kauna na da kuma girmama ni. Yayi kuka yana roko na. Amma ban canza ra’ayi na ba. Na gaya masa ya goge lamba na a wayar sa! Yanzu ina da kwanciyar hankali. Ina iya zuwa ganin abokai na. Nayi kewar su sosai. Sai anjima.

Kuna tare da wani dake raunata ku? Dan Allah kuyi magana kamar Sophie. Kada ku bari wani ya saka ku jin kamar baku da daraja. Dukkan mu na cancancin kasancewa da mutane dake da hankali. Ku rarraba labarin ku da abokan ku. Muna da karfi tare.

Kun san wata kamar Sophie? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback