Yadda zaku kaunar iyalin ku

Amara ta rarraba yadda ta koya kaunar iyalin ta

Iyalina shine komai na. Yan uwa na ne abokai na. Bazan iya tunanin rayuwata bada iyali na ba.

Kaunar iyali na bai kasance iya kan haka ba a koda yaushe.

Ina nufin cewa ban taba fahimta muhimmanci iyali sai a shekarar daya wuce.

A shekarar daya wuce wasu yan mata biyu a al’ummar mu suna tsangwama ni.

Koda yaushe suna tsokana na. Suna kira na mummuna da katuwa. Wata rana suka wasa mun ganyen ayaba a jiki.

Wannan ya saka ni bakin ciki sosai. Na zub da tabbaci a kai na. Ina tsoron fita waje.

Babban yaya na ta lura canji a halayye ne.

Tayi mun magana akan sa. Na gaya mata akan masu tsangwama na.

Ta gaya mun kada na yarda mutane kamar su su saka ni bakin ciki.

Ta kai rahoton su a wajan iyayen mu da yan uwan mu.

Mahaifiyata tayi mun magana akan tsangwama. Tace na koya yin magana idan ana tsangwama na

Tace kada na dogara akan maganar mutane domin farin ciki na.

Mahaifiyata tayi wa iyayen su magana akan sa.

Dan uwa na yace na nuna masa yan matan. Ya musu kashedi su kyale ni.

Daga baya kuma dan uwa na ya gaya mun na kai rahoton kowane mutum daya tsangwama ni. Naji kauna da tsira.

Na koya abubuwa kadan daga wannan masaniyar. Koda yaushe ku kai rahoto a wajan wani amintaccen mutum idan ana tsangwamar ku ko kuwa kun fuskance wani al’amari da baku ji tsira ba. Kada ku saka ra’ayin wani akan ku ya danganta da yadda kuke ganin kanku. Zaku iya koya akan tsangwama anan

Duk da yadda nake da ban haushi wasu lokuta, iyali na na kan so na.

Iyali ya koya mun kula da. Na kasancewa mafi inganci wa kai na da sauran mutane.

Gaya mana abun da kuke kauna akan iyalan ku a sashin sharhin.

Share your feedback