Yadda zaku samu abokai

Toyin ta bada labari akan yadda ta samu abokai

Suna na Toyin. Shekaru na goma sha biyar.

Mahaifina ya rasu a shekarar daya wuce. Domin goyon bayan iyali na ina kwashe lokaci ina taimakon mahaifiya ta a shagon ta.

Kuma ina halarta wani makarantar abinci so biyu a sati.

Bana samun lokacin yin wani abu wa kai na. Wasu lokuta ina ji kamar bani da abokai. Ina kunyar kusanta mutane.

Kwanan nan naje gidan wata yar uwa ta. Tana tadi da kawarta dana shiga. Sunyi kamar sun shaku sosai. Abokantakar su ya jima.

Wannan ya saka ni tunani ko zan taba samun abokiya kamar haka.

Na tambaye ta yadda ta samu abokiya kamar haka.

Ta bani wasu shawara masu kyau. Tace nayi kokarin kashe kunya na.

Sai ta bani wani aiki da kuma wasu shawara. Tace;

Zabi wata da shekarar ku daya a makarantar abincin ku sai ku fara magana. Zaku iya farawa ta gabatar da kanku. Ki tambaye ta akan ranar ta. Ki tambaya ko tana jin dadin makarantar. Ki tambaye ta abubuwa kamar “Menene kika tsara zaki yi bayan makarantar?” Ni ina son na fara wani karamar sana’a, ke fa?”. Ki gwada wannan kowane rana da mutane dabam.

Idan wata tsaran ki tazo shagon. Kiyi mata fara’a. Zaki iya tadi da su akan wakoki ko bidiyo dake yayi.

Amma kiyi hankali. Ba kowa bane zaki iya abokantaka da.

Idan zaku zabi wasu da zaku yi wa magana, kuyi kokari ku zabi tsaran ku. Kuyi musu magana a fili. Ku guje wajaje da ba mutane ko kuwa wani waje da zai hana ku walwala.


Na gwada shawarar da yar uwata ta bani kusan kowane rana. Na lura cewa daya daga cikin yan matan aji na ta fara mun fara’a. Wasu lokuta tana zuwa wajan da nake zama tayi labari dani.

Wasu kwanaki muna labari da juna a Facebook.

Nayi murna samun abokiya. Ina fatan zan kara samun karin abokai.

Kuna neman samun abokai? Ku gwada wasu dabarun Toyin. Kuna da abokai? Gaya mana yadda kuka zama abokai.

Share your feedback