Yadda hauwa ta samu farin ciki kuma
Da nake shekaru goma sha uku na fara zama da Yar uwar mahaifi na da yaran ta.
Ina jin dadin zama da yar uwar mahaifi na. Amma wasu lokuta ina jin kamar bata so na.
Tana fadin abubuwa da yawa dake sa ni bakin ciki.
Ina samu karin hukunci daga wajan ta fiye da nata yaran.
Tana kira na mara sauri, ko mara amfani, ko kuwa katuwar banza.
Tana kira na “bakutuwa” sai tace ba abun dana sani sai cin abinci. Tace shiyasa ni doluwa ce.
Kowane lokaci ina tsoro idan ina kusa da ita. Ina i’ina idan ina magana da ita.
Kalmomin ta na shafi na.
Suna saka ni jin kamar bani da amfani. Wasu lokuta ina jin kamar tana da gaskiya.
Ina ganin kamar halayyar ta dai dai sanda na ziyarta abokiya ta Mariam.
Naga yadda yar uwar mahaifiyar ta ke mata fada ba tare da kalmar zagi ba. Na tambaye ta idan wannan dai dai ne.
Tace yar uwar mahaifiyar ta bata taba amfani da kalmomin zagi a kan ta ba. Na gaya mata akan yar uwar mahaifi na da abubuwan da take fadi mun.
Tace wannan halin ba daidai bane.
Tace ana cin zarafin shauki na. Tace bai kamata wani yasa ni ji kamar bani da amfani. Ta bani shawara nayi magana da yar uwar mahaifi na akan shi.
Na gaya mata ina tsoron yin mata magana.
Ta gaya mun nayi wa yar uwar mahaifiyar ta magana. Dana same ta ta bani shawara akan abun yi.
Tace “ Ni ba mara sauri bace, ko mara amfani, ko kuwa katuwar banza. Tace ni gagaruma ce. Tace na cigaba da gaya wa kai na haka. Idan ina jin haushi na dauki hankali na da abubuwa dake kawo mun farin ciki. Tace na gaya wa yar uwar mahaifi akan abubuwan da take mun. Tace kada na yarda kalmomin ta su dame ni.
Idan ina jin bakin ciki kuma ina son na bayyana yadda nake ji, ina rubutu domin na taimake kaina jin dadi. Ina ajiye wani mujalla da nake rubuta baiti na wakoki. Wasu lokuta ina jin sauti. Suna taimako na kara jin dadi.
Kwanan nan na samu karfin zuciya na gaya wa yar uwar mahaifi na yadda nake ji. Tayi mamaki. Ta roke gafara akan halayyar ta.
Yar uwar mahaifi na nada hankali da kalmomin ta yanzu.
Kema zaki iya tsira daga abubuwan dake halakar dake. kada ki yarda wani masanayi guda daya ya shafi rayuwar ki na gaba.
Akwai wata abokiyar ki ko kuwa wani baligin mutum daya taimake ki bi da al’amari masu inkari kamar wannan? Dan Allah ki rarraba labarin ki a shafin sharhi.
Share your feedback