Ina kaunar sa, amma ban shirya yin soyayya ba

Komai nada lokacin sa

Ban taba sha’awar wani yaro ba sanda na hadu da Nonso. Nan take na san cewa ya banbanta da sauran samari. Baya tafiya a kungiya kamar sauran samari a ungwan mu. Yana rike kansa da kyau– Koda yana nan shi daya ko da abokan sa. Bana ji yana daga muryan sa. Kuma, yana da kyau sosai.

Wata rana, wata makwafciyata ta gaya mun cewa wani yaro a ungwan mu na takura mata. Nonso ya bashi kashedi ya daina raunata ta ko kowace yarinya. Da yake magana, sai naji dadi a cikin zuciya na. A nan ne na san cewa ina son sa.

Tunda ban taba kaunar wani yaro ba, ban san abun yi ba. Bani da wanda zan yi wa magana. Sai na yanke shawara na guje Nonso. Tun da dai bai san ni ba. Ya za’a yi ya kula da ni? Sai wani abun mamaki ya faru. Makwafciyata tace Nonso na damun ta akai na da dadewa! Yana son ya sani ko zamu iya zama abokai. Ta gaya mishi cewa tayi mun magana akan sa domin ta sani ko ina son sa. Abun ya bani mamaki.

Duk da haka dai, ta gabatar damu sai muka fara magana. Naji kamar mun saba da magana. Dukkan mu biyu na son irin abubuwa daya kamar kamshin kasa bayan ruwan sama. Yana da annashuwa da kyau, saboda haka bana gajiya da labari dashi. Amma kun san me ya jawo mun hankali? Wani ma’adanin wakoki daya hada mun! Wannan ne kyauta mafi kyau da wani ya taba bani.

Ina kaunar abokantakar mu sosai, musamman tunda ban shirya yin soyayya ba. Wasu tsaran mu na yin soyayya, amma yana bani tsoro kuma kamar akwai wahala sosai. Ina son na kara sanin kai na kafan na fara yin soyayya da wani. Na zata haka nonso ma ke tunani. Shiyasa dayace yana so na, abun ya bani mamaki sosai.

Bana son na gaya masa a’a domin ina tsoro zan bata abokantakar mu. Bana son nayi tunanin asarar sa. Amma kuma, bana son na fita dashi ko kowa. Ba yanzu ba dai.

A karshe, na gaya wa Nonso cewa ban shirya yin soyayya ba. Nayi masa bayani cewa ina son na dauke lokaci ba tare da matsi ba. Na bayana masa cewa bana son nayi soyayya domin kowa nayi. Nonso ya amince dani. Yace yana girmama ra’ayi na kuma zamu iya cigaba da abokantakar mu. Idan abun ya bata mishi rai, bai nuna mun ba.

Bayan nan, abubuwa suka dawo daidai. Nonso bai kara mun maganar kuma ba, wannan ya kara saka ni girmama shi. Wannan masaniyar ya koya mun cewa ina da karfi fiye da nake zato. Na tsaya da gaske, kuma ku ma zaku iya yi.

Menene tunanin ku akan soyayya? Ku rarraba da mu!

Share your feedback