Ina ganin mahaifiyata bata kauna na

Idide ta bamu labarin ta

Da nake karamar yarinya, kowa na fadin cewa ina kama da mahaifiyata. Sunce ina da wushiryar ta da kuma launin fatar jikin ta. Wasu na fadi cewa tafiyar mu da muryan mu daya ne. Wannan ya saka mahaifiyata farin cikin sosai. Tana kira na tagwayen ta. Amma sai komai ya canza dana cika shekaru goma sha biyar.

Mahaifiyata ta fara fushi dani kowane lokaci. Ta daina labari da dariya dani. Bata godiyar duk abun da nake yi. Idan nayi wanke-wanke, zata nema wani datti a kwanon tayi masifa akai. Idan nayi sharan gida, zata nema wani waje da datti tayi magana akai. Rayuwa yayi mun wuya. Wasu lokuta ina kuka kafan nayi bacci.

Sai kuma mahaifiyata ta hana ni kwashe lokaci da abokai na. Tace ba abokan arziki bane. Nayi kokarin na canza mata ra’ayi. Amma tayi mun ihu.

Abokai na suka daina zuwa gidan mu. Kuma ni ma na daina ziyarta su da amsa sakonnin rubutun su. Sai suka share ni. Bani da kowa da zan iya yin wa magana. Harda mahaifiyata. Ina zaman kadaici.

A wani karshen mako, kawar mahaifiyata Inna Queenie ta zo gidan mu. Ina son ta sosai don tana da hankali. Da mahaifiyata ta shiga daki ta dauka wani abu, Inna Queenie ta tambaye ni ko ina lafiya. Na girgiza kai na da farko. Bana son komai ya kai kunnuwan mahaifiyata. Amma naji kamar zan iya dogara da Inna Queenie. Sai na gaya mata komai.

Inna Queenie tace kada na damu. Ta bayana mun cewa mahaifiyata na masaniyar abubuwa da yawa yanzu. Ba’a biya ta albashin ta ba na watani da yawa. Abubuwa sun yi muni har mai gidan mu na barazanan korin mu daga gidan.

Inna Queenie ta tabbatar mun cewa mahaifiyata na kauna na sosai. Tace ina girma da sauri, kuma mahaifiyata bata san yadda zata jimre ba. Ta roke ni na kara bawa mahaifiyata dama. Na yarda.

Na fara yin kokarin aikin gida sosai. Bayan lokaci kadan, mahaifiyata ta daina yin korafi. A maimako, ta fara yaben aikin da nakeyi. Har ta bari na kitsa mata gashi dana tambaye ta– kamar yadda nake yi da nake karama.

Kadan kadan, muka fara yin magana. Ta yi furta cewa ta zata na bar ta wa abokai na ne. Na bata hakuri. Na gaya mata ba wanda zai iya daukan matsayin ta a rayuwata. Sai ta rungume ni ta bani hakuri ita ma.

Yanzu abubuwa sun kara inganta. An biya mahaifiyata albashin ta kuma mai gidan mu ya daina damun ta. Ni kuma abokai na sun dawo mun. Duk da haka, idan ina da matsala, ina zuwa wajan mahaifiyata ne. Koda menene, zata cigaba da zama tagwaye na.

Kuna shiri da mahaifiyar ku ko kuwa wata babba yar dangin ku dake kula da ku? Gaya mana a sashin sharhi.

Share your feedback