An kore ni daga makaranta

Yadda tasiri mara kyau ya saka ni cikin matsala

Ina aji daya a makarantar sakandare da aka kore ni. Zan iya tuna da ranar daya faru.

Na kasa zuwa gida. Ina tsoron fuskanta mahaifina. Na tabbata cewa zai mun duka.

Naji tsoro sosai har sai naje gidan ‘yar uwa ta. Dabara na shine na boye a wajan na dogon lokaci.

Na tuna na rokar ‘yar uwar na kada ta gaya wa kowa musamman mahaifin mu. Tace na zabi tsakanin komawa gida na gaya musu abun daya faru ko kuwa kiran su a waya mu gaya musu.

Na yarda na gaya musu da kaina.

Da nake tafiya gida da hankali a ranar, naji kamar duniyar zata nade.

Sa’ar al’amarin shine, mahaifina baya gida ranar dana kai gida. Na bawa mahaifiyata wasikar kora na. Na gaya mata abun daya faru. Nayi kuka sosai. Ya dauke ta lokaci sosai kafan ta iya lallashi na.

Na kwashe lokaci sauran ranar a daki na ina kuka.

Washe gari mahaifina ya tambaye ni meyasa ban je makaranta ba. Ina ganin mahaifiyata bata gaya masa ba.

Ban san yadda zan gaya masa ba. Yace zai kai ni makaranta. A wannan lokacin, na san cewa dole na gaya masa.

Ina kuka, na gaya masa an kora yara kusan ishirin daga makaranta domin wani taro daya faru a makarnata. Abun mamaki a maimakon ya mun duka ya lallashe ni.

Sai yace mun; Wannan ba karshen rayuwar ki bane. Na san ki sosai. Ke ‘Yar ta ce kuma nasan kina da natsuwa. Amma naji bakin ciki da aka kore ki.

Wannan darasi ne miki kiyi hankali da mutanen da kike kira abokai. Ta nan baza ki shoga matsala ba. Ki koya daga wannan kuskuren nan. Kuma kada ki damu, zamu saka ki a wani makaranta.


Kalmomin mahaifina ya saka hankali na ya dan kwanta. Amma, ina bakin ciki a wannan lokacin. Ina zaman gidan a yayin da sauran tsarana na makaranta.

Duk da haka, na koya abubuwa da yawa da nake gida. Na koya muhimmancin samun mutane kusa daku da zasu goya muku baya a lokuta masu wuya. Kuyi tunanin abun da zai faru da iyali na sun juya mun baya.

Kuma na koya nayi hankali da mutane da nake kira abokai. Kuga abun daya faru dani. Sakamakon kwashe lokaci da kungiya mara kyau ne a lokacin da bai dace ba.

Shawara na wa kowa dake karanta wannan shine ku koya daga kuskure na. Ku kula da abokan ku. Ku tabbata cewa mutane ne masu dabi’u kamar ku. Yakamata ku ajiye abokai da zasu taimake ku kara inganta kanku.

Idan abokan ku na yawan saka ku a cikin matsala kuna bukatan sabobin abokai. Kuna al’ajabin yadda zaku samu abokan kwarai? Ku karanta wannan makalar akan Yadda zaku gina abokantaka masu tsira.


Kun taba samun kanku a cikin wani matsala saboda wata abokiya ko kungiyar abokai? Ku gaya mana abun da kuka yi a sashin sharhi.

Share your feedback