Nayi aure da nake budurwa

…...Amma duk da haka na cimma muradi na

Suna na Ruth kuma ina budurwar dana zama amarya! Bayan dana kammala makarantar sakandare, iyaye na suka saman mu mijin aure.

Da farko, ina nishadi, amma sai rayuwa na ya zama na yau da kullum: farkawa da safe, shirya mai gida na zuwa aiki, yin aikin gida, cin abinci da kuma komawa bacci.

“Haka rawuya na zai cigaba ko zan iya cimma muradina na za zama malama?” Koda yaushe ina tunanin haka.

Wani yamma bayan abincin dare, na ja mai gida na zuwa wani waje da muke son zuwa mu kwashe lokaci. Na gaya masa akan muradina na zama malama. Ya ki yarda, yace aiki zai mun yawa. Magana yayi tauri, muka kasa cimma yarjejeniya. Na yanke shawara bazan daga murya na ba ko kuwa na cigaba da gardamar.

Na yanke shawara na tamabaye mahaifiyata ta bani shawara.

Mama na tace aure ba gadon wardi bane. Wasu lokuta mutane basu amince da juna, musamman idan yazo wajan mata da bin muradin su. Duk da haka, kada ya hana ki yin magana akan sa.

Ta bani shawara na nema wani hanya da zan saka mai gida na ya ga amfanin cimma burina. Ga misali, zan iya goyon bayan iyali na da kudi. Zan iya fahimta wahalar aikin sa da kyau, kuma na basa shawara. Kuma tunda muna karban albashi tare zamu iya ajiye kudi wa rayuwar na gaba.

Mahaifiyata ta bani dabarun nan guda uku na tattauna maganganu masu wuya.;

  1. Ki tabbata cewa kin yi sa a waje mai shiru
  2. Ki fara da magana da kowa ke so domin maganar yayi sauki
  3. Ki bayyana sarai abun da kuke so. Ki tuna kada ki daga muryan ki idan maganar bai je a yadda kike tsammani ba.

Na dauki shawarar mahaifiyata. Nayi wa mai gida na magana. Yace zai kara tunani akan sa. Bayan lokaci kadan, ya canza ra’ayin sa, ya bani goyon baya.

Yanzu na san cewa idan kuna da muradi zaku iya cimma koda bayan aure ne. Idan kuna tare da mutum daya dace zai baku shawara kuma ya goya muku baya.

Me zai hana ku cimma burin ku? Ku gaya wa Babban Yaya a sashin sharhi.

Share your feedback