Shakara na farko a matsayin uwa

Yandda nake kokarin cimma burina

Shekaru na goma sha shida dana dauke ciki.abun ya bani mamaki,yakamata n ice mai hilkima mai cin jarabawa a makaranta amm g ani a nan da ciki.

Na ji tsoron gaya wa mahaifiyata. Na ji kamar na kunyata ta.

Eh, tayi fushi sosai kuma nayi bakin ciki wannan al’amarin, amma bata yanke alaka dani ba, ko kuwa ta kore ni.

A gaskiya, abun da take so shine rayuwa mafi kyau wa ni da yaro na.

Da farko, kasancewa uwa ya zo da dan wuya. Daga rashin bacci da dare, zuwa hukunci daga mutane a ungwan mu.

Amma, mahaifiyata ta taimake ni daidaita da canjin.

Ta saka komai game da zama uwa ya mun sauki.

Kowane lokaci tana kokarin karfafa gwiwa na. Tana tunatar dani cewa haihuwa a wannan shekarun ba karshen rayuwa na bane. Tana son na kara inganta kai na. Na cimma burina, na zama mai kwarewar kwamfuta.

Ta Har karfafa ni na dauke wani darasi.

Bisa ga mahaifiyata, ina bukatan shirya kaina da kwarewa da zai bani damar samun kudi

Saboda haka, na shiga wani makarantar kwamfuta dake kusa da gidan mu. Kuma na fara daukan wani darasin tsarin dokokin kwamfuta da yazo a kyauta a yanar gizo gizo. Na dauke darasin domin ya taimake ni zama mai kwarewar kwamfuta. Kuma bada jimawa ba, zan iya taimakon mutane gina shafin yanar gizo gizo da kuma aikace-aikacen wayar hannu.

Shekara daya ya wuce tun dana zama uwa kuma a gaskiya, kasancewa uwa shine abu mafi kyau daya faru da ni.

Na koya yadda zan karfafa kaina, kara tabbaci, da kuma musamman, yadda zan yi kaunar kaina koda menene. Yanzu, ba abun da zai iya hana ni.

Ina godiya wa goyon bayan mahaifiyata.

Na kosa na zama mai kwarewan kwamfuta wata rana! Saboda na iya samun kudin kwarai na lura da mahaifiyata da kuma yarinya na. *

Wanne matsaloli ne kuka shawo a kwanan nan? Ku gaya mana a wajan sharhi a nan kasa.

Abun ya bani mamaki.

Yakamata ni ce mai hikima, mai cin jarabawa a makaranta, amma ga ni a nan da ciki.

Ta Har karfafa ni na dauke wani darasi.

Bisa ga mahaifiyata, ina bukatan shirya kaina da kwarewa da zai bani damar samun kudi

Share your feedback