Abokiya ta na bakin ciki

Nnenna ta gaya mana yadda ta taimake abokiyar ta

Shekarar abokiyata Ngozie goma sha biyar. Abokantakar mu ya kai shekaru biyar yanzu. Mahaifiyata nada shago a kusa da shagon mahaifiyar ta. Muna kwashe lokaci tare sosai.

A watani kadan da suka wuce Ngozie ta canza. Ta fara aikata wasu halayye. Ta daina zuwa kasuwa kamar yadda ta saba. Har ta daina daukan waya na ko amsa sakonnin rubutu na a facebook.

Sai wata rana na yanke shawara naje na ziyartar ta. Dana gan ta tana cikin bakin ciki. Bata magana kamar yadda ta saba.

Nake ta tambayan ta menene matsalar, amma taki ta mun magana. Na gaya mata bazan tafi ba sai ta gaya mun abun dake damun ta.

Sai ta bude baki ta gaya mun

“Mahaifina yace na aura shugaban wajan aikin sa. Wannan mutumin nada mata uku. Mahaifina yace wanna auren zai bamu daman taimakon iyalina. Shugaban yayi masa alkawari cewa zai tura yan uwa na makaranta kuma ya biya mana bukatun mu idan na yarda na aure sa. Dani da mahaifiyata nata rokan sa ya soke auren. Amma yaki saurarren mu.”

Naji wani irin dana ga abokiyata na bakin ciki. Ina son na ta taimaka. Sai nayi wa iyaye na magana.

Da suka ji labarin ta, mahaifina ya yanke shawara yayi wa mahaifin Ngozie magana.

Ya gaya masa yadda aure da sauri zai shafe jikin Ngozie da kuma shaukin ta.

Ya basa shawarar sauran hanyoyi da zai iya taimakon iyalin sa. Ya gaya masa ya horas da Ngozie a wani sana’a. A ta nan zata samu wani kwarewa da zata yi amfani ta samu kudi.

Bayan lokaci kadan mahaifin Ngozi ya dakatar da auren. Yace zai tura ta makarantar koyar yin takalma.

Yanzu abokiyata Ngozie na makarantar koyan yin takalma. Na lura cewa tana farin cikin yanzu.

Bata daina mun godiyar taimakon dana mata ba.

Kuna al’amari daya da Ngozie? Kuyi magana. Ku fara da gaya wa iyayen ku yadda kuje ji. Idan kuna son yayi muku sauki, ku fara yin gwajin abun da zaku gaya musu kafan ku fuskance su. Zaku iya rubuta shi ma. Kuma ku nema lokacin da basa komai kuma zaku samu hankalin su.

Zaku iya yin wa wani ko wata dake kusa da iyayen ku magana. Ku tambaye su su taimaka suyi wa iyayen ku magana.

Da kune Nnenna me zaku yi dabam? Kuna da abokai dake al’amari daya da Ngozie? Kuyi mana magana akan sa a sashin sharhin mu.

Share your feedback