Kusa ko nesa, abokai har abada

Wa yace rashin gani shine fitar hankali?

Suna na Nneka. Nayi girma da abokiya ta Lillian a farfajiya daya. Na girme ta da shekara daya, amma wannan bai hana mu zama abokai ba. Muna zuwa ko ina kuma muna yin komai tare. Muna karasa maganar juna. Mutum daya baya cin abinci sai dayan yaci.

Farkon shekaran daya wuce, anyi wa mahaifi na sauyi zuwa wata jiha. Wannan yana nufin cewa dukkan iyalin mu zasu koma wajan. Munyi bakin cikin wannan al’amarin. Mun yi musayar warwaron abokantaka. Mun yi wa juna alkawari cewa zamu cigaba da tuntuba juna.

Da farko, bai zo da sauki ba. Sanda na saba da sabon rayuwa na. Amma da zaran dana samu na sasanta kaina, abubuwa suka daidaita. Abun yayi kamar ban tafiya ba.

Muna kiran juna da tura sakon rubutu wa juna. Muna tura hotuna kuma muna tura mahadar yanar gizo gizo na labarai masu dadi. Wasu lokuta muna samun labarai da yawa mu tura wa juna. Zamu tura sakon rubutu da cikakken kwatance. Duk lokacin da Lillain ta tura sakon rubuta akan wani al’amari mai ban dariya, ina jin kamar ina wajan.

Duk da nesan, mun cigaba da abokantakan. Lokacin da Lillian ta sa kai a cibiyar al’ummar ta, ta fara gaya mun. Lokacin dana hade wani kungiyar waka, Lillian ta taimake ni zabi suna.

Kan lokaci muka yi abokantaka da wasu mutane. Amma duk da haka mun cigaba da maganar juna wa mutanen nan. Wani lokaci, nayi kuskure na kira sabon abokiya ta da sunnan Lillian. Dana gaya wa Lillian, Muna ta dariya.

Yanzu muna ajiya domin zuwan Lillian. Lillian na murna. Bata taba barin jihar ba. Tana son ta ga dukkan wajajen nan masu ban mamaki a hotuna na. Nima Ina kirga kwanakin. Na kosa na nuna wa Lillian wajaje. A karshe abokai zasu hadu kuma.

Koda kuna nesa daga wasu abokan ku, zaku iya cigaba da tuntuba juna. Daga kiran waya zuwa yin hira, Waya yasa sadarwa ya kara sauki.

Yaya kuke hulda da abokan ku dake wasu wajaje? Ajiye sharhi a nan kasa.

Share your feedback