Labarin Amaka mai sha’awa
A gida, ana jin murya na fiye dana kowa. Zan iya fitar da kai na daga wani al’amari da magana. Na san abun fadi kuma lokacin da zan fada. Amma a makaranta, ni daban ce. Ina da kunya da kuma tsoro. Ana tswangwama na, kuma ina jin kunya sosai bana iya gaya wa kowa.
Komai ya canza da Linda tazo makarantar mu. Ita ce gajeruwar ajin mu. Bata magana in bai zama dole ba. Bada jimawa ba, masu tswangwamar suka fara. Wata rana, suka kama ta suka fara tsokanan ta. Amma bata yi kuka ba. Ta tsaya ta kala kowane daga cikin su a cikin ido. Tayi tafiyar ta da kan ta a sama.
Masu tswangamar suka yi mamaki. Ba abun da suka zato ko tsammani bane. Basu san abun yi ba. Yadda Linda da dauke kanta ya bani karfin hali. Na gaya wa kai na idan zata iya yi, nima zan iya yi. Dana kai gida, nayi gwajin abun dana koya a gaban madubi. Na tunatar da kaina na jarunta.
Da farko, yayi kamar masu tswangwamar sun manta dani. Sai suka kewaye ni a lokacin wasa. suka kira ni sunaye, suka ta mun dariya. Na ja nunfashi domin na natsu. Na tura kirji nace wa kaina kada na yarda abun da suka fada akai na ya dame ni saboda ba haka nake ba. Na gaya musu idan baza su iya mun magana da mutunci ba kada su damu su mun magana gaba daya. Na gaya musu idan basu daina zolaya na ba zan kai rahoton su a wajan wani babban mutum.
Bayan nan, masu tswangwamar suka daina damu na. Na kara zama tabbaciya. Na fara yin magana a makaranta. Nayi abokiya da Linda. Dana gaya mata ita ba bani sha’awa na samu karfin hali, tayi murmushi kamar ba komai bane.
Wasu lokuta zaki samu kanki a wani al’amari mara kyau ko mai wuya. Kada kiji tsoro kiyi magana. Muryan ki ne babban makamin ki. Idan kina ji kamar ana miki barazana ko kuwa firgita, ki gaya wa wani babban mutum da kika yarda da nan take.
Kin taba kare kanki? Gaya mana labarin ki a nan kasa.
Share your feedback